Karamomin Waliyyai



“Na kasance ina ganin hasken wahayi, sannan ina jin kanshin annabta, sannan na ji karar shaidan yayin da wahayi ya saukar wa Manzo. Sai na tambayi Manzo cewa: Wannan kara ta wacece? Sai ya amsa mini da cewa, wannan kara ta shaidan ce, ya yi wannan kara ne sakamakon yanke kauna da ya yi a kan cewa wani zai bauta masa. Ali! duk abin da nake gani kai ma kana ganinsa, sannan abin da nake ji kai ma kana jinsa! kawai sai dai kai ba Manzo ba ne, amma kai ne wazirina, kuma zaka kasance a cikin hanya mikakkiya”[8].

Karfin da zai sanya mutum ya iya ganin mala’iku yana kuma jin wata murya da ba a saba ji ba, wannan yana nuna karfin ruhin mutum ne, wanda yake samuwa ta hanyar bautar Allah. Manzo (s.a.w) Kur’ani ya bayar da shedar cewa, yana ganin mala’iku da jibril. Ganin Jibril yana bukatar karfin ruhi da kammala ta musamman, ta yadda zai ba mutum damar ya iya ganin wannan abin halitta.

A cikin matayen Bani Isra’il maryam ce kawai Allah ya bai wa wannan damar ta ganin mala’ika, lokacin da wannan mala’ika yake yi mata albishir da cewa ba tare da dadewa ba zata samu da, duk wannan ya faru ne sakamakon kamalar ruhi da maryam (a.s) ta kasance tana da shi.

6-Samun Ikon Yin Wani Abu A Cikin Duniya

Sakamakon bautar Allah ba kawai jiki ne zai kasance karkashin ikon mutum ba, duniya ma zata kasance tana bin umurninsa, ta yadda ta hanyar izinin Ubangiji sakamakon karfin ruhin da ya samu ta hanayar kusancinsa ga Allah, yana iya sarrafa duniya ba tare da yin amfani da wani abu da aka saba yin amfani da shi ba, ta yadda zai kasance ya mallaki mu’ujiza da karamomi.

A nan domin kafa hujja a kan bin da muke magana a kansa, ya kamata mu kawo wasu ayoyi da suke tabbatar da hakan cewa waliyyan Allah bisa wasu dalilai na musamman suna tare kuma da izinin Allah suna iya yin wani abu a cikin duniyar halitta ba tare da amfani da wani abu da aka saba amfani da shi wajen yin wannan abin.

Kur’ani wajen bayyanar da karfi da mu’ujizar da annabawa suke da ita wacce take da tushe daga kudrar Ubangiji marar iyaka, ya kawo kissoshi daban-daban, amma a nan zamu kawo wasu daga cikinsu kamar abin da ya shafi labarin annabi Yusuf, Sulaiman, Da Isa (a.s) zamu yi magana a kansu a takaice kamar haka:

A-Mu’ujizar Annabi Yusuf Da Warkar Da Babansa

Kur’ani yana cewa: Annabi Yusuf (a.s) ya aika wa babansa da riga ta hanyar wani wanda Kur’ani yake ambata da “Bashir” ya ce masa ka jefa wannan rigar bisa fuskar babana Yakub (a.s) zai samu ganinsa kamar yadda ya kasance a da, wannan dan aike bayan ya share hanyar da ke akwai tsakanin Misra dakan’an ya jefa wannan riga ga fuskar annabi Yakub sakamakon haka ne ya samu lafiya ya koma yana gani. Kur’ani mai girma yana bayyanar da wannan al’amari cikin ayoyi guda biyu kamar haka:

1-“Ku tafi wannan rigan tawa ku jefa ta a kan fuskar babana zai koma yana gani. “[9]



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 next