Girmama Kaburbura Masu TsarkiKur’ani mai girma[3] yana siffanta hasken Ubangiji da fitila mai haske ta yadda yake haske kamar tauraruwa. A ayar da take biye wa wannan aya kuwa ya nuna cewa wurin wannan haske yana gidajen wasu mutane masu girma wadanda suke ambaton Allah a ciki safiya da yamma.[4] A cikin wannan aya jimalr da take cewa “Ana tasbihinsa safiya da yamma, tana nuna dalilin da ya sa aka daukaka wadannan gidajen wadanda aka ambata a cikin ayar da ta gabata. A ayar da take biye mata kuwa an siffanta masu yin ibada a cikin wadannan gidaje ne, inda yake cewa: “Mutane ne wadanda kasuwanci ba ya shagaltar da su daga ambaton Allah da tsayar da salla, domin suna jin tsoron ranar da zukata da idanu suke jujjuyawa suna tsorata.[5] Wannan aya tana bayani ne a kan girma da daukakar gidajen da ake zikirin Allah ake kuma tsarkake shi a cikinsu. A nan dole ne mu yi bayani a kan abubuwa guda biyu kamar haka: 1-Me ake nufi da gidaje a cikin wannan aya? Masu tafsiri sun yi sabani a kan ma’anar wannan ayar ta yadda kowane ya dauki daya daga cikin ma’anonin kasa: A-Ana nufin gidaje a cikin wannan aya da masallatai guda hudu. B-Ana nufin dukkan masallata ne a cikin wannan aya. C-Ana nufin gidajen Manzo ne. D-Masallatai da gidajen Manzo. A cikin wadannan ma’anoni da aka ambata a kasa ma’ana ta uku ce kawai zata iya daidai kamar yadda zamu kawo dalilai da suke karfafa hakan.
|