Girmama Kaburbura Masu TsarkiC-Yada maganganunsa da abin da ya rubuta. D-kiyaye kayan tarihin da suka shafe shi. D-Girmama Kabarinsa da yin gini domin kiyaye shi daga lalacewa. Aikata wadannan abubuwa da makamantansu wadanda suke sun halasta a musulunci, yin su ga Manzo da iyalan gidansa ya nuna kauna ne a gare su. Tirmizi yana ruwaitowa a cikin sunan dinsa: “Manzo (s.a.w) ya kama hannun Hasan da Husain sai ya ce: Duk wanda yake so na ya kuma so wadannan yara guda biyu da babansu da mamansu, to zai kasance a matsayina a ranar kiyama.[19] Kowannenmu ya san da cewa babban jikan Manzo yana rufe ne a “Bakiyyaâ€, sannan mai biye masa yana rufe a Karbala, Sannan wadannan wurare kodayaushe suna ganin al’ummar musulmi masu ziyara, saboda haka duk wani gini kowane abu wanda za a yi domin kiyaye wadannan wurare, nau’i ne na nuna soyayya ga wadannan jikoki na Manzo kuma bin umurnin Manzo ne a kan soyayya gare su, kamar yadda muka yi bayani a ruwayar da ta gabata. A yau al’ummu da dama suna kokari wajen tunawa da manyan tarihinsu (kamar sojoji da ‘yan siyasa da wadanda suka yi wasu ayyuka na gyara) ta hanyoyi daban-daban, sakamakon haka ne suke halarta jana’izarsu yadda ya kamata. Sannan su rufe a wani wuri na musamman a karkashin gini mai kawatarwa, ta yadda wadanda zasu zo a nan gaba kamar yadda na yanzu suke kulawa ta musamman a kan su, suma su yi kulawa da girmamamawa ta musamman a kan wadannan manyan mutane. Don haka mu ma musulmi dole mu yi kokari don yin gine-gine da zasu kare kabuburan manyan mutanenmu. Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org – www.haidarcip.org Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP) Facebook: Haidar Center - December, 2012
|