Ziyarar Kaburbura Masu Daraja



 Sai Manzo ya ce: “Ki ce amincin Allah ya tabbata ga nutanen wannan gida daga musulmai da muminai, Allah ya gafarta wa wdan da suka riga mu da wadanda zasu zo bayammu. [14]

Wurin da ake kafa dalili a nan shi ne wajen koyar da A’isha yadda ake ziyara, saboda haka idan ya zamana mace bai halitta ba ta ta ziyarci makabarta, a nan babu ma’ana Manzo ya koyar da matarsa.

 Sannan bugu da kari A’isha ta kasance tana gaya wa sauran mata dangane da abin da ya auku, saboda haka da wannan zamu iya gane cewa ya hada kowa da kowa cewa ziyarar baki daya ta halatta ga mace da namiji. Domin kuwa matar Manzo da sauran mata duk daya suke a wajen hukuncin Allah.

2-Fadima (a.s) ‘yar Manzo (s.a.w) kuma daya daga cikin mutanen mayafi (wadanda aka saukar da aya ta 33 suratul ahzab a kansu) Bayan wafatin Manzo ta kasance tana ziyartar kabarin amminta wato shahidin Uhud inda take yin salla raka’a biyu sannan ta yi kuka a kabarinsa.

 Hakim Nishaburi bayan ya ruwaito wannan ruwaya yana cewa: wadanda suka ruwaito wannan ruwaya dukkansu amintattu ne kuma adalai, ta wannan fuskar ba su da bambanci da maruwaitan Bukahri da Muslim. [15]

 3-Tirmizi ya ruwaito daga Abdullahi Bn abi malika yana cewa: Lokacin da Abdurrahman Bn Abibakar ya rasu a wani wuri da ake kira da (Hubsha) Sai aka dauki jana’izar shi zuwa Makka a ka rufe shi a can. Bayn wani lokaci sai A'isha wadda take ‘yar uwa ce a gare shi ta zo Makka domin ziyarar kabarin Abdurrahaman dan’uwanta, Sannan ta yi wasu wakoki guda biyu wadanda suke nuna tsananin damuwarta a kan rashinsa. [16]

4-Bukhari yana rubuta cewa: Wata rana Mnazo ya ga wata mata gefen wani kabari tana kuka, sai ya ce mata “Ki mallaki kanki sannan ki yi hakuri a kan rasa wani naki da kika yi”. [17]

 Amma bukhari bai ruwaito cigaban wannan hadisi ba, amma Abu Da’ud a cikin sunan dinsa ya cigaba da wannan hadisi ga abin yake kawowa: Wannan mata ba ta gane Manzo ba, sai ta kalubalanci Manzo ta ce: Me ya dame ka dangane da abin da musibar da ta same ni?

 A wannan lokaci sai wata mata da take gefenta ta ce mata kin gane kuwa wannan kowane ne?, Manzon Allah ne (s.a.w).

A wannan lokaci wannan matar domin ta gyara abin da ta yi wa Manzo sai ta tafi gidan Manzo ta ce masa: Ya manzon Allah ka yi hakuri ban gane kai ne ba. Sai Manzo ya amsa mata da cewa: Hakuri a cikin musibar da ta samu mutum shi ne abin da ya dace. [18]



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next