Ziyarar Kaburbura Masu Daraja



 Saboda haka idan haka ne ma’anar wannan jumla zata kasance kamar haka: Har abada kada ka tsaya a kan kabarin Munafukai.

 Sakamakon haka ne zai zamana munafukai sun rasa wannan falala su kuwa muminai suna rabauta daga wannan falala, domin kuwa Manzo yana iya halartar kabarin muminai lokacin rufe su ne ko kuwa lokacin ziyara domin ya yi musu addu’a.

 

Ziyarar Kabari A Cikin Sunnnar Manzo

 Bayan ruwayoyi guda biyu da muka kawo farkon wannan bahasi wadanda suke nuna hikimar ziyara, dole a nan mu kara fadakarwa a kan cewa, Manzo da kansa ya kasance yana zuwa makabartar “Bakiyya” domin ziyartar kaburburan musulmi. Sannan a kasa tarihi ya tabbatar da hakan kamar haka:

1-Musulim a cikin sahih dinsa yana cewa: An ruwaito daga A’isha cewa duk karshen dare yakan tafi makabarta domin ziyara, duk lokacin da ya shiga wannan wuri yana ce musu:

 â€œAmincin Allah ya tabbata gareku ya gidan mutane muminai kun samu abin da ake alkwari da zuwansa a gaba, Kuna rayuwa tsakanin mutuwa da tashin kiyama, mu ma zamu hadu daku, Ya Allah ka gafarta wa wadanda suke a cikin” Bakiyya”.

2-Muslim a cikin Sahih dinsa ya ruwaito daga A’isha tana cewa Manzo ya ce mata: Jibril ya sauka zuwa gareshi ya ce masa Allah yana ba da umarni da cewa ku tafi ziyarar mutanen “Bakiyya” Sannan ku nema musu gafara.

 A’isha tana cewa: Sai na tambayi Manzo cewa, yaya za yi musu addu’a? Sai Manzo ya ce ki ce: “Amincin Allah ya tabbata a gareku yaku mutanen wannan gida daga muminai da musulmai, Allah ya jikan wadanda suka riga mu da wadanda zasu zo bayanmu daga cikinsu, Mu ma insha Allah muna nan zuwa mu hadu da ku”. [11]

3- Muslim yana ruwaitowa daga Buraida cewa: Manzo (s.a.w). ya kasance yana koyar da Sahabbansa cewa yayin ziyara ga abin da zasu ce: “Amincin Allah ya tabbata a gare ku ya ku mutanen wannan gida muminai muna nan zamu hadu da ku, Muna rokon Allah da ya ba mu lafiya tare da ku.[12]



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next