Bidi’a A Cikin Addini



Daya daga cikin abubuwan da suka kawo bidi’a a cikin addini shi ne, ta’assubanci (riko da abu) marar dalili a kan al’adun iyaye da kakanni, da kuma al’adun da mutum ya tashi a cikinsu. Tsananin soyuwar da mutum yake da shi dangane da wadannan abubuwan yakan sanya shi ya yi nesa da fahimtar gaskiyar addini ta yadda zai mai da bata a mai makons gaskiya.

Tarihi yana nuna cewa: Mutanen Da’ifa sun aiko mutane zuwa ga Manzo domin su wakilce su domin su su bayyana wa Manzo shirinsu domin karbar addinin musulunci, amma sai suka sanya wa musulunci sharudda guda kamar haka:

1-Ya zamana ya halasta musu riba.

2-Ya halasta musu kusantar matan banza.

3-Wuraren bautar gumakansu su kasance har zuwa shekaru uku masu zuwa.

Lokacin da Manzo ya samu labarin wadannan sharudda nasu sai ya nuna tsananin damuwarsa kuma ya nuna rashin amincewar da ko daya daga cikinsu. [19]

Idan da mutanen Da’ifa sun kasance musulmii na hakika, to dole ne su mika wuyansu ga hukuncin Ubangiji, ba wai su gabatar da son zuciyarsu ba a kan musulunci. Wannan a fili yake sakamakon manufofinsu daban-daban ya sanya suka sanya wa addinin wadannan sharudda. Daga cikin neman da suka yi kuwa na ci gaba da bautar gumaka, wannan kuwa duk ya faru ne sakamakon ta’assubanci marar dalili.

Wadannan dalilai guda uku na sama da wadansu makamantansu su ne tushen bidi’o’i a cikin addini. Sannan akwai wasu dalilai ma bayan wadannan amma saboda karancin damar da muke da ita zamu takaita a nan.

 

Fito Na Fiton Addini A Kan Hana Bayyanar Bidi’a



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 next