Bidi’a A Cikin AddiniHaka nan hadisin manzoma ya nuna cewa bidi’a daya daga cikin mafi munin abubuwa ce, sannan tana kaiwa zuwa ga halaka kuma ta kai mutum zuwa ga fushi da zabar Allah. 6-Hankali ma yana karfafa wannan tir da Allah wadai da shari’a take yi wa bidi’a. Zuwa nan mun fahimci ma’nar “bidi’a†a lugga da ma’anar a shari’a, a nan zamu yi nuni da wasu abubuwa na gefe kamar haka. Kashe-Kshen Bidi’a Zuwa Gida Biyu Daya daga cikin kashe-kashen da ake yi wa bidi’a shi ne a kan kasa ta zuwa bidi’a mai kyau da marar kyau (hasana da sayyi’a). Asalin wannan kasa bidi’a zuwa mai kyau da marar kyawu kuwa yana komawa ne zuwa ga halifa na biyu (Umar Bn Khattab). Saboda mutanen har zuwa shekara 14 bayan hijira, sun san cewa ana yin sallar nafila ta watan azumi a daidaiku ne (Sallar tarawihi). Amma sakamakon wasu dalilai a zamaninsa aka yi wannan salla a cikin jam’i da limanci Ubaiyu Bn Ka’ab a cikin masallacin Manzo. Lokacin da halifa na biyu ya ga wannan al’amari sai ya ce “Madalla da wannan bidi’aâ€. A nan ba zamu shiga cikin maganar cewa shin wannan sallar nafila a daidaiku ne za a yi ta ko kuwa a cikin jam’i ba, kawai a nan muna magana ne dangane da kasa bidi’a zuwa mai kyau da marar kyau wanda ya samo asali ne daga halifa na biyu. A bayanimmu na baya mun ga cewa ma’anar bidi’a ita ce zuwa da wani sabon abu a cikin addini wanda babu shi, sannan babu wani dalili na shari’a da yake nuni a kan hakan. A kan haka ne bidi’a ba zata taba zama wani abu daban ba sai marar kyau, saboda haka kasa bidi’a zuwa mai kyau da marar kayu sam ba shi da wata ma’ana. Koda yake da mutane zasu kawo wani abu sabo a cikin yanayin rayuwarsu amma ba su dangana shi ba zuwa ga Allah to wannan abin zai iya daukar ma’anar lugga ta kalmar bidi’a, sannan za a iya kasa ta zuwa gida biyu mai kyau da marar kyau. Wato; al’adun da suke bullowa a cikin al’ummu daban-daban suna iya kasuwa zuwa masu kyau da marasa kyau. Domin kuwa da yawa daga cikinsu suna iya zama masu amfani ko kuma su zamo mararsa amfani. Amma bidi’a a shari’a guda daya ce kuma dukkanta marar kyau ce kuma ba ta halatta. (Wato kirkiro wani abu sabo a cikin addini wanda babu shi, sannan kuma babu wani dalili na shari’a a kan yin hakan). Dalilan Canza Wasu Abubuwa A Cikin Addini Duk da cewa hakikanin musulunci ba wani abu ba ne sai kawai mika wuya ga Allah, sannan wasu daga cikin akidu na aikace sun samo asali ne daga wannan mika wuyan, saboda haka ta yaya ne mutum musulmi zai iya canza wani abu a cikin addini, Sannan menene nufinsa da dalilinsa a kan yin hakan?
|