Girmama Kaburbura Masu Tsarki 2Saboda haka dukkan wadannan hadisai suna bayyanar mana da ma’anar Kalmar Musharrafan da ta zo a cikin hadisi, ba tana nufin kasancewar kabari ya yi bisa ba daga kasa ko kada ya yi, tana nufin shi kansa kabarin kada ya kasance yana da tudu kamar bayan rakumi. 3-Nabawi kan sharhin wannan hadisi yana cewa: Bai kamata ba kabari ya yi bisa da kasa ba ko kuma ya zamana ya yi tudu kamar bayan rakumi. Ya cigaba da cewa dole ne bisansa ya kasance kamar kamun hannu guda sannan samansa ya zamana a baje ba mai tudu ba.[17] 4-Kurdabi acikin tafsirinsa ya ruwaito wannan hadisi da a ka ambata yana cewa: Wannan hadisi abin yake nunawa shi ne baje kabari shi ne Sunna, sannan yi masa tulluwa bidi’a ne.[18] 5-Ibn Hajar askalani bayan ya yi bayani a kan mustahabbancin baje saman kabari yan rubuta cewa: Hadisin Abi Hayyaj ba yana nufin cewa ba a baje ya zama daidai da kasa, abin da yake nufi shi ne a baje saman kabari ta yadda za a daidaita shi babu wani tudu a samansa, duk da yake cewa ya dan yi sama da kasa.[19] Kamar yadda wasu ba su ba wannan bayani muhimmanci ba, (mu dauka ma wannan hadisi yana nufin cewa a baje kabari ta yadda zai zama daya da kasa babu wani tudu) kafa hujja da shi a kan rusa gine-ginen da aka yi a kaburburan bayan Allah, zai fuskanci matsaloli guda biyu: 1-Baje kabari ta yadda zai zama daya da kasa babu wani tudu ya sabawa dukkan ra’ayin fukaha domin kuwa dukkansu sun tafi a kan haka din cewa mafi karanci tashinsa ya kai kamun hannu guda.[20] 2-Idan muka dauka cewa wannan hadisi yana nufin cewa a baje kabari ta yadda zai zama daidai da kasa, to dole ne mu rusa kabari ta yadda zai zama daya da kasa, ba wani gini da aka yi ba a saman kabarin. Saboda haka sam wannan hadisi ba yana magana ba ne a kan ginin da yake kan kabari yana magana ne a kan shi kansa kabarin! Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org – www.haidarcip.org Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP) Facebook: Haidar Center - December, 2012
|