Girmama Kaburbura Masu Tsarki 2



 

Hasumiyoyi Masu Tsawo A Garin Makka

 Ibn Jubair yana bayyana yadda garin Makka ya kasance da hasumiyoyi masu daukaka a kan kaburbura a garin Makka, wanda ambatonsu a nan zai janyo mu tsawaitawa. Akwai wurare kamar Maulidin Nabi, Maulidin Zahara da Darul Khaizaran (wurin ibadar Manzo na sirri).

 Sannan ya ambaci wurare masu girma na sahabbai da tabi’ai a Madina, A cikin wannan kuma yake ambatar Raudhar Abbas Bn Ali Bn Hasan Bn Ali (a.s) wanda yake da gini mai tsayi a garin Madina. Sannan ya cigaba da bayyana yadda wadannan wurare suke.

 Idan muna so mu fadi duk abubuwan da Ibn Jubair ya gani a garuruwan Sham da Iraki na sahabbai da manyan bayin Allah zai janyo mu tsawaita a cikin hakan, don haka muna iya wadatuwa da wannan. Saboda haka wanda yake so ya samu Karin bayani sosai a kan haka sai ya koma zuwa ga wannan littafi na sa.[4]

 Ibn Najjar (578-643)[5] Muhammad Bn Mahmud wanda aka fi sani da Ibn Najjar wanda yake shi ma shahararren musulmi mai yawon shakatawa ne a cikin littafinsa “Madinatur Rasul” yana cewa:

 â€œAkwai wata dadaddiyar hasumiya mai tsawo a farkon makabartar “Bakiyya”wadda take da kofofi guda biyu wanda kowace rana ake bude daya daga cikinsu domin masu ziyara.[6]

 Wadannan suna daga cikin littattafan tafiye-tafiye da muka dauko daga cikinsu, sannan ana iya komawa zuwa ga wasu littattafai na tafiye-tafiye wadanda suke tabbatar da yin gine-gine a kaburburan annabawa da bayin Allah wani abu ne da yake sannane kuma wata Sunna ce mai tsawon tarihi a tsakanin masu kadaita Ubangiji.

 Ibn Hajjaj Bagdadi (262-392) wanda yake mawaki ne shararre a iraki ya yi wata kasida ta yabon Imam Ali (a.s), sannan ya yi wannan kasida ne a haramin Imam Ali (a.s) acikin taron mutane, a farkon wannan kasida ga abin yake cewa: “Ya kai ma’abocin wannan hasumiya fara a garin Najaf duk wanda ya ziyarce ka kuma ya nemi ceton Allah daga gareka to Allah zai karbi cetonsa”.

 Wannan baiti yana nuna cewa kabarin Imam Ali (a.s) a farkon karni na hudu ya kasance yana da hasumiya.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 next