Tafiya Domin Ziyarar Kabarin Manzo (s.a.w)



Jawabain wannan tambaya kuwa a fili yake domin wannan amsa tana matsayin gabatarwa ce domin aiwatar da aikin mustahabbi, saboda haka a akidar wasu malamai tana matsayin mustahabbi, wasu kuwa suna cewa tana hukunci “Mubah” ne. Duk yadda ta kama kasantuwar wannan tafiya domin aiwatar da mustahabbanci ce ba zata taba zama haramun ba. Domin kuwa ba zai inganta ba a hankali Allah madaukaki ya umurce mu da aikin mustahabbi na ziyartar Manzo sannan ya haramta abin da yake matsayin gabatarwa ne domin aiwatar da wannan aikin. Saboda haka daga nan muna iya gane cewa hukuncin wannan tafiya domin aiwatar da wannan aiki ta halitta. [1]

 Kamar yadda yake a tarihi shi ne musulman da suke rayuwa a sauran sassan duniya wato ba wadanda suke rayuwa ba a garin Madina sukan taure kayansu domin tafiya zuwa ziyarar kabarin Manzo mai girma a nan ga wasu misalai a kan hakan:

 Bilal wanda yake mai kiran salla ne na Manzo kuma Manzo ya kasance yana kaunarsa. Bayan tafiyar Manzo ya zabi ya tafi wani wuri yiwa musulunci hidima, sakamakon haka ne ya yi hijara daga garin Madina. Wani dare sai ya ga Manzo a cikin mafarki yana ce masa: Wannan wane irin rashin kulawa ne Bilal? Yanzu lokaci bai yi ba da zaka ziyarce ne?

 Lokacin da Bilal ya tashi daga barci yana cikin bakin cikin da ya mamaye masa zuciya, sai kawai ya tanaji abubuwan bukata domin yin tafiya kuma ya tafi zuwa Madina. Lokacin da Bilal ya shiga a cikin Raudar Manzo yana kuka da murya mai karfi a wannan hali ya dinga goga fusakarsa a kan kabarin manazo. A nan haka sai kwatsam abin kauanar Manzo wato Hasan da Husain (a.s) sai suka yi wajensa sai ya kama su ya runguma, sai suka ce masa, Muna tsananin son mu ji muryar kiran sallarka, kiran sallar da kake yi wa kakanmu manzon Allah (s.a.w).

 Bilal lokacin sallar Asubahi sai ya hau wurin da ya kasance yana kiran salla a zamanin Manzo (s.a.w). ya kira salla.

 A lokacin da kira sallarsa ya mamaye Madina Ya girgiza garin Madina a wannan lokaci. A lokacin da ya yi kalmar shahada a cikin kiran sallarsa sai duk mutane suka daga murya suna kuka, a lokacin da kuwa ya yi shahada a kan manzancin Manzo (Ashhahadu anna Muhammadar Rasulullah) ai sai duk mutanen Madina suka yo waje suna kuka, kamar yadda ake rubutawa bayan ranar da Manzo ya yi wafati madina ba ta taba ganin irin kukan da ta gani ba a wannan lokaci.[2]

 2-Umar Bn Abdul Aziz ya kasance yana hayar mutane domin su taho daga Sham zuwa madina domin su yi masa sallama ga Manzo.

 Subki a cikin Futuhus Sham yana rubuta cewa: Lokacin Umar Bn Abdul Aziz ya yi Sulhu da mutanen Kods sai Ka’abul Akhbar ya shigo wajen kuma ya musulunta, a wannan lokaci Umar ya ji dadi kwarai da musuluntarsa.

 Sai Umar ya ce masa: Kana iya bi na mu tafi madina mu ziyarci kabarin Manzo ta yadda zamu fa’idantu da ziyararsa?

 Sai Ka’ab ya amsa wa khalifa abin da ya nema daga gareshi, ya yi shirin tafiya tare da khalifa. A lokacin da Umar ya shiga garin madina, farkon abin da ya fara yi shi ne ya shiga masallacin Manzo ne domin ya yi wa Manzo sallama.[3]



back 1 2 3 4 5 6 7 next