Tafiya Domin Ziyarar Kabarin Manzo (s.a.w)Wannan kafa hujja ta Ibn Taimiyya kuwa idan muka lura da kayu zamu iya gane rashsin ingancinsa, domin kuwa ba shi da kafafuwa masu karfi. Domin kuwa mun san cewa jumlar da take kebewa tana ginuwa daga sassa guda biyu kamar haka: 1-Jumlar da ake kebewa daga gareta: “Ba wanda ya zo wurina†2- Jumlar da a ka kebance “Sai Ali†Hadisin da ya gabata ya ginu ne ta hanyar jumloli biyu ne. 1-jumla ta farko jumlar da aka kebance daga gare ta “Kada ku yi tafiyaâ€. 2-Jumla ta biyu kuwa, wadda a ka kebance. “Sai masallatai ukuâ€. A jumlar ta farko abin da aka kebance bai fito ba a fili, bisa la’akari da ka’dar larabci a nan dole mu kadda wata jumla, wadda zata iya zama daya daga cikin wadannan jumloli guda biyu kamar haka: 1-Mai yiwuwa ka iya cewa “masallaci†ne. (Wato kada ka yi tafiya zuwa kowane masallaci sai masallatai guda uku) 2-Mai yiwuwa ana nufin “wuri†ne (kada ka yi tafiya zuwa wani wuri sai masallatai guda uku).
|