Ziyarar Kabarin Manzo Mai Girma Hadisi na farko: “Wanda duk ya ziyarci kabarina aljanna ta wajaba a gareshiâ€[23]. wannan hadisi Allama Amini ya ruwaitosa tare da sanadi daga littafi 41. Hadisi na biyu: Dabarani a cikin mu'ujamul Kabir, Gazali a cikin ihya'u ulum daga Abdullahi Bn umar, Manzo yana cewa: “Duk wanda yazo ziyara kuma saboda kawai ziyarata ya zo, to ya wajaba in cece shi a ranar kiyama. “ Hadisi na uku: Darul kutni ya ruwaito daga Abdullahi Bn umar cewa Manzo (s.a.w) ya ce: Duk wanda ya ziyarce ni bayan wafatina alokacin aikn hajji, to kamar ya ziyarce ni a lokacin da nake a raye. “ Hadisi na hudu: Darul kutni ya ruwaito daga Bn Umar cewa Manzo (s.a.w) ya ce: “Duk wanda ya ziyarci kabarina kamar ya ziyarce ni a lokacin da nake a raye. “ Anan ya kamata mu yi nazarin matsayin ziyara a wajen Imaman Ahlul-bait (a.s): Ziyar Manzo A Ruwayar Ahlul-Bait (a.s) 1-Imam Bakir (a.s) yana cewa Manzo (s.a.w) yana cewa: “Duk wanda ya ziyarce ni ina raye ko bayan na yi wafati zan kasance mai cetonsa a ranar kiyamaâ€[24] 2-Imam Ali (a.s) yana cewa: “Ku cika hajjinku da manzon Allah a lokacin da kuka fito daga dakin Allah, domin kin ziyararsa rashin girmamawa ne gare shi, an umurce ku da yin hakan. Tare da ziyarar kaburburan da aka umurce ku zaku karashe hajjinku. “ 3-Imam Sadik (a.s) daga manzon tsira (s.a.w) yana cewa: “Duk wanda ya zo Makka don aikin hajji amma bai ziyarce ni ba, zan banzatar da shi a ranar tashin kiyama, wanda kuwa ya ziyarce ni cetona ya wajaba a garesa, duk wanda cetona ya wajaba a garesa, aljanna ta wajaba a gareshi. Saduk: Ilalish shara'i'i 4-Imam Sadik (a.s) yana cewa Manzo. (s.a.w) yana cewa: “Duk wanda ya ziyarce ni zan zama mai cetonsa a ranar tashin kiyamaâ€. [25]
|