Ziyarar Kabarin Manzo Mai Girma



 Saboda haka ne malaman Tafisri suka tafi akan cewa, girmama Manzo bai kebanci lokacin rayuwarsa ba, saboda haka dole ne a kiyaye shi har bayan rasuwarsa. Harma ayar da ke umurta musulmi da su rika magana a hanakali a gaban Manzo, tana nan a matsayinta, inda Allah yake cewa: “Ya ku wadanda kuka yi Imani kada ku daga muryarku saman muryar Annabi[19]“.

 Saboda haka bai kamata mutum ya rika magana da karfi a cikin haramin mazon mai tsaira ba. Sannan wannan aya an rubuta ta a kan kabarin Manzo, wanda duk ya je wannan wuri ya gane wa idonsa hakan.

B: A Mahangar Sunna

 Mun ga hukunci da matsayin Kur’ani akan wannan al'amri yanzu abin da ya rage shi ne ku ga kuma me Sunnar Manzo ke cewa a kan hakan..

 Ruwayoyi da dama sun zo akan wannan magana ta ziyarar kabarin Manzo, kuma malamai sun yi kokarin tattara su da kuma tabbatar da danganensu. Saboda haka anan a matsayin misali zamu kawo wasu daga cikinsu kamar haka:

1-Takiyyuddeen subki (ya yi wafati a shekara ta756h) a cikin littafinsa “Shifa'us sikam” ya ruwaito hadisi tare da sanadi ingantacce. [20]

2-Nuruddin Ali Bn sahmudi (ya yi wafati 911H) ya ruwaito ruwaya 17 akan wannan magana, a cikin littafinsa na tarihin Madina sannan kuma ya inganta sanadinsa.[21]

3-Muhammad fukki daya daga cikin Malam Azahar tare da shafe sanadi ya ruwaito matanin ruwayoyi 22 akan ziyarar Manzo. [22]

4-Allama Amini tare da tare da bin diddigi wanda ya ci a yaba masa, ya tattara ruwayoyi da dama akan ziyarar Manzo (s.a.w) saboda haka anan kawai zamu yi nuni da daya daga cikin ruwayoyi da ya samo daga littafi 41 da a ka ruwaito a kan hakan. Al-Gadir

 Saboda haka kawo dukkan ruwayoyin da danganensu ba zai yiwu ba a nan, saboda haka kawai anan zamu takaita ne da kawo wasu kawai daga cikinsu. Wadanda suke son Karin bayani sai su koma zuwa littafin da aka ambata a sama.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 next