‘Yan Shi'a Na Farkob- Ibn Khaldon yana cewa: Wasu jama’a daga sahabbai suna goyon bayan Ali kuma suna ganin shi ya cancanta fiye da waninsa, yayin da aka ba wa waninsa sai suka ki hakan, suka kuma ji takaici sai dai saboda sun riga sun kafu cikin addini da kuma kwadayinsu a kan hadin kai, ba su dada a kan haka ba sai ganawa da kuma kyama da jin takaici[4]. c- Ibn Hajar a littafin Isti’ab: yana fada game da bayanin Ibn Dufail: Amir dan Wasila dan Kinana Allaisi Abud Dufail ya samu shekaru takwas daga rayuwar Annabi (s.a.w) kuma an haife shi a shekarar Uhud kuma ya mutu a shekara ta dari, yana cewa: Shi ne karshen wanda ya mutu daga wadanda suka ga Annabi (s.a.w) kuma ya ruwaito kusan hadisai hudu, ya kasance mai son Ali kuma daga sahabbansa a dukkan yakokinsa, kuma amintacce ne kuma yana ganin fifikon shaihaini (Abubakar da Umar) sai dai yana ganin Ali (a.s) ya fi su[5]. Bayan dukkan wadannan bayanai ina son in dan karkato da hankulanmu cewa yayin da nake karanta littattafan tarihi ban ga wani lokaci ba duk da yake yana da tsawo a duk fadin rayuwar halifofi da na samu wani ya yi zagi daga sahabban Imam Ali (a.s), kuma sai dai kawai akwai wanda ya yabi halifofi akwai kuma wanda ya yabi Imam Ali (a.s) hatta da masu tsananin riko da wilayar Ali ba mu samu wanda ya zagi wani ba daga wadanda suka gabatar da Imam Ali game da halifanci. Abul’aswad Addu’uli yana cewa: Ina son Muhammad so mai tsanani Da Abbas da Hamza da wasiyyi Kaskantattu Banu Kushair suna cewa Tsawon zamani kada ka manta da Ali Ina son su saboda son Allah har sai
|