Faruwar Shi'anci



A nan ina son in juyo tunanin Dakta Ahmad Mahmud zuwa ga cewa Shi'a ba sa kafa dalili a kan Shi’anci da samuwar Shi’anci a lokacin Annabi (s.a.w) da abin da ya zo daga gareshi a hadisansa, mas’alar kamar yadda masu ilimin usul ne suke kiran ta da cewa: Tana matsayin doka ce ba wani abu wanda yake samamme a waje ba, wato ba dole ba ne a same su a wannan lokaci kamar yadda shi Dakta Ahmad Mahmud yake nunawa.

Wadannan siffofi ne da Annabi (s.a.w) ya ambata ga Shi'a kuma ko’ina ne aka same su kuma kowane zamani ne. Amma kafa dalili a kan cewa akwai Shi'a a lokacin Annabi (s.a.w) to ana iya fahimtarsa daga ruwayoyi da kuma karinoni masu yawa da a kan iya kawo su game da wannan al’amarin. Wadannan kuwa Dakta Abdul’aziz Adduri ya kawo wani bangare daga cikinsu, kuma ya kawo madogararta[17], tare da wasu bayanai da kuma wani kaidi da ya kawo kan cewa Shi’anci na ruhi da gina al’umma ne ake nufi a wannan lokaci akwai shi kamar yadda ya kawo a cikin wani bangare na dalilansu wanda a kan haka ne kuma Yahaya Hashim Fargal ya tafi a littafinsa[18].

Wasu daga wadannan ra’ayoyi suna komawa ne tun farko zuwa ga lokacin da Shi’anci ya bayyana a rayuwar Annabi (s.a.w) yayin da wasu jama’a suka fifita Ali (a.s) a kan waninsa na daga sahabbai kuma suka rike shi shugaba kuma jagora wadanda suka hada da Ammar dan Yasir, da Abuzar gifari, da Salman Farisi, da Mikdad dan Aswad, da Jabir dan Abdullah da Ubayyu dan Ka’abu, da Abu Ayyub Al’Ansari, da Banu Hashim[19], da sauransu.

Don haka ne ma yake kuskure ne wani ya kawo bayyanar Shi’anci da cewa ya zo bayan wannan lokaci na Annabi (s.a.w) tare da samuwarsu tun a lokacin Annabi mai tsira da aminni. Muhammad Abdullah yana fada a cikin littafinsa na "Tarihul Jam’iyyatus Sirriyya" gun bayaninsa da ta’alikinsa a kan abin da wasu littattafan tarihi[20] suka ruwaito yayin da Annabi (s.a.w) ya tara danginsa yayin saukar fadinsa madaukaki: "Ka gargadi danginka makusata", Shu’ara’: 214. Sai ya kira su zuwa ga biyayya gareshi ba su amsa masa ba, sai Ali (a.s) ne kawai ya amsa masa, sai ya yi riko da wuyan Ali (a.s) ya ce: Wannan dan’uwana ne, kuma wasiyyina, kuma halifana a cikinku sai ku ji daga gareshi kuma ku bi shi.

Muhammad Abdullah ya yi ta’aliki da cewa: Yana daga kuskure a ce: Shi’anci ya faru ne tun farko a lokacin da Khawarijawa suka ware daga rundunar Imam Ali (a.s), Shi’anci ya fara ne tare da bayyanar lokacin isar da sakon Annabi (s.a.w) yayin da aka umarce shi da ya yi gargadi ga danginsa makusanta a wannan aya.

Daga Littafin Sheikh Wa'ili Na HAKIKANIN SHI'ANCI

Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id da Munir Muhammad Sa'id


[1] Tarihin Ibn khaldon: J 3, shafi: 364.

[2] Fajarul islam: Shafi: 266.

[3] Tarihul islam: J 1, shafi: 371.



back 1 2 3 4 next