Faruwar Shi'anci Na biyar: Mustashrik Julad Tasihar ya ce: Shi’anci ya fara ne bayan wafatin Annabi (s.a.w) kuma kai-tsaye bayan al’amarin Sakifa[6]. b- Ra’yin da ya tafi a c- Ra’ayin da yake ganin an kafa Shi’anci ne lokacin halifancin Imam Ali (a.s) kuma daga wadanda suka tafi a kan wannan ra’ayi akwai Nubkhati a littafinsa na "Firakus Shi'a"[8] da Ibn Nadim a littafin "Alfihrast", yayin da ya ayyana lokacin faruwar Shi’anci da yakin Basara da kuma abin da suka gaba ce ta, na al’amuran da suka yi tasiri kai-tsaye wajen habakar jama’ar Shi'a da kafuwarsu[9]. d- Ra’ayin da ya tafi a Yayin da kuma Dakta Abdul’aziz Adduri ya tafi a Wannan shi ne ra’ayin Buruklman a cikin tarihin al’ummun musulmi yayin da yake cewa: A bisa gaskiya mutuwar shahada da Imam Husain (a.s) ya samu kuma ba ta da wani tasiri na siyasa kamar yadda yake rayawa- ta taka babbar rawa wajen samun ci gaban addini gun Shi'a rundunar Ali (a.s), wanda ya zama bayan haka ne mahadar jayayyar dukkan Larabawa –kuwa wannan ba haka yake ba- kuma yau kabarin Husain (a.s) a Karbala yana daga cikin mafi tsarkin wuri gun Shi'a, musamman Farisawa da ba su gushe ba suna ganin babban burinsu yana cikin tattaruwa gunsa[12]. Wannan ra’ayi na Buruklman hada da cewa yana da wata dasisa da ya kunsa haka nan ya saba wa mafi girman abin da masu fadin ra’ayoyi game da bayyanar Shi’anci sakamakon kashe Imam Husain (a.s) yayin da suka tafi a kan cewa an samu kafuwar siyasar mazhabar Shi’anci bayan wannan waki’a ne, yayin da shi Buruklman yake ganin babu wata hakikanin gaskiya ta siyasa a cikin wannan waki’a, al’amarin da ya kasance musu ne ga abin da yake sananne karara. Kuma wasu mutane sun goya wa Buruklman baya a wannan ra’ayi kamar Yahaya Fargal a cikin littafinsa[13], da cewa wannan ra’ayoyi hudu da suke bayanin faruwar Shi’anci ba zasu iya tsayawa ba kyam gaban dalilin da yake rusa su, kuma ba ina nufin in gaggauta raddinsu ba, da sannu zan ambaci ra’ayi na biyar wanda da shi ne zai iya tabbatar da cewa wadannan ra’ayoyi suna dogara ne da abubuwan da suka faru wadanda suke bayanin cewa Shi’anci ya kafu ne sakamakon tasirantuwa da wasu abubuwan da suka faru wadanda wadannan ra’ayoyi suka dogara da shi a tarihin da suka kawo na bayyanar Shi’anci sai suka yi tsammanin an same shi a wannan lokacin, alhalin an same shi ne a tun farko. A yanzu lokaci ya yi da zamu kawo maka ra’ayoyin jama’ar Shi'a musamman masana daga cikinsu, daga cikinsu akwai: e- Ra’ayin Shi'a da wasunsu na daga marubuta a wasu mazhabobin. Yayin da wasu suka tafi a kan cewa an samu Shi’anci ne lokacin Annabi (s.a.w) kuma Annabi (s.a.w) da kansa ne ya dasa irinsa ta hanyar hadisai da suka zo a harshen Annabi (s.a.w) kuma suka ba wa Ali (a.s) matsayi a wurare daban-daban da suka rauwaito, hada da cewa akwai amintattu daga malaman Sunna da suka ruwaito kamar Suyudi a ruwayarsa daga Ibn Asakir gun tafsirin ayoyin nan biyu ta shida da ta bakwai daga surar Bayyina da sanadinsa zuwa ga Jabir dan Abdullah da ya ce: Mun kasance gun Annabi (s.a.w) sai Ali (a.s) ya gaba to, sai Annabi (s.a.w) ya ce: "Na rantse da wanda raina take hannunsa wannan da shi’arsa su ne masu rabauta ranar kiyama: Sai aka saukar da fadin Allah madaukaki "Hakika wadanda suka yi imani suka kuma yi aiki na gari su ne fiyayyun talikai". Kuma Ibn Udayyi ya karbo daga Ibn Abbas cewa ya ce: Yayin da aka saukar da fadin Allah madaukaki "Hakika wadanda suka yi imani suka kuma yi aiki na gari su ne fiyayyun talikai". Sai Annabi (s.a.w) ya ce da Imam Ali (a.s) kai ne da Shi'arka. Kuma Ibn Mardawihi ya karbo daga Imam Ali (a.s) cewa, manzon Allah (s.a.w) ya ce: Shin ba ka ji fadin Allah (s.w.t) ba cewa "Hakika wadanda suka yi imani suka kuma yi aiki na gari su ne fiyayyun talikai". To kai ne da kai da shi’arka kuma alkawarin inda zan hadu da ku shi ne tafki, yayin da al’ummu zasu zo domin hisabi, to kai za a kira ku haskaka masu fararen alamomi[14], don haka ne ma Abu Hatim Arrazi ya tafi a kan cewa kalmar Shi’anci shi ne farkon suna da ya bayyana a cikin musulunci, kuma wannan lakabi ne da ake gaya wa hudu daga sahabbai da suka hada da Abuzar da Ammar da Mikdad da Salman Farisi, kuma bayan yakin Siffaini wannan lakabi ya shahara ga masu goyon bayan Imam Ali (a.s)[15]. Wadannan hadisai da suka gabata wadanda Ibn Asakir da Ibn Udayyi da Ibn Mardawihi suka ruwaito, kuma bayanin Ahmad Mahmud Subhi ya biyo bayansu a littafinsa na "Nazariyyatul Imama" yana cewa: Wadannan hadisai da suka zo a harshen Annabi (s.a.w) game da Imam Ali (a.s), ba sa nuna cewa akwai wata jama’a a lokacin Annabi (s.a.w) da tabayyana mai suna Shi'a kamar yadda dai Annabi (s.a.w) ya yi ishara da bayyanar khawarijawa da marikawa kamar yada yake ce wa Imam Ali (a.s): Zaka yaki Nakisin (A’isha su dalha da zubair) da Kasidin (Mu’awiya) da kuma Marikin (Khawarijawa). Kuma bai nuna akwai su ba a matsayin wata jama’a wacce take da akidu mabambanta ko wasu fikirori daban[16].
|