Faruwar Shi'anci
Yaushe Shi’anci Ya Fara
A bayanan da suka gabata mun tabbatar da cewa Shi’anci abu guda ne a da can da kuma yanzu, kuma samun ci gaban da yake faruwa a mas’alolinsa ba komai ba ne sai dai fikirorin da suka bubbugo daga asalinsa. Kuma da karin wasu babobin da suke samuwa sakamakon alakokin wadannan fikirori da kuma hada wasu mas’aloli da wasunsu da a A yanzu zamu koma zuwa ga farkon Shi’anci da kuma asalinsa faruwarsa da nuna yadda yake haduwa da cewa shi ne hakikanin musulunci. Sannan kuma sai mu ga yadda yake tun farkon samuwarsa da kuma yadda aka samu share fagen kasancewarsa, kuma shin ya faru ne sakamakon ayyukan tausayi ko soyayya, ko kuma sakamakon ayyuka ne masu dogaro da hankali da masu rikon wannan mazhabi suka yi riko da shi bisa tirjiya da dagewa kan wahalhalu suna masu fadaka da hakan. Idan muka koma wa wadannan al’amuran da aka saba a cikinsu muna masu bibiyar abin da masu bahasi suka fitar da abin da ya rigaya, da kuma dukkan abin da suka rinjayar a bahasinsu, to dole ne mu gabatar da wasu misalai na wasu ra’ayoyi a wannan fagage wadanda zasu kasance tanadaddu, sannan sai mu bar wa mai karatu fage domin ya fitar da hakikanin gaskiya da kansa, ya kawo wani ra’ayi nasa da zai yi kokarin da ya kasance ya dogara bisa ilimi. Yayin da masu tarihi da bincike suke iyakance lokacin faruwar Shi’anci suna iyakance shi ne da lokacin da ya fara tun lokacin Annabi (s.a.w) ne, karshensa kuma ya kare da lokacin da aka kashe Imam Husain (a.s), kuma zamu kawo maka wasu daga ra’yoyinsu, sai mu bar maka nawa ra’ayi a karshen fasali. a- Ra’ayin da suke ganin Shi’anci ya fara daga lokacin wafatin Annabi (s.a.w), kuma wadanda suka tafi a Na farko: Ibn Khaldon: Yana cewa: "Shi’anci ya bayyana yayin da Manzo Muhammad (s.a.w) ya yi wafati sai Ahlu-baiti (a.s) suka ga su ne suka fi cancanta da wannan al’amari kuma halifanci yana ga mazajensu ne banda wani daga kuraishawa, kuma yayin da wasu jama’a daga sahabbai suke mika jagoranci da biyayya ga Imam Ali (a.s) kuma suna ganin shi ne ya fi cancanta a kan waninsa yayin da suka ga an kauce masa zuwa ga waninsa sai suka ki yarda da hakan..."[1]. Na biyu: Dakta Ahmad Amin ya ce: Farkon irin da ka shuka Shi’anci da shi su ne wadanda suka ga cewa bayan wafatin Annabi (s.a.w) Ahlu-baiti (a.s) su ne suka fi cancanta da halifancinsa fiye da wasunsu[2]. Na uku: Dakta Hasan Ibrahim ya ce: Ba mamaki, a bisa hakika musulmi sun yi sabani bayan wafatin Annabi (s.a.w) game da wanda zai yi halifanci bayansa, sai dai al’amarin ya tuke da jagorancin Abubakar wanda ya kai al’umma ta kasu gida biyu na jama’ar al’umma masu yawa da kuma ta Shi’anci[3]. Na hudu: Ya’kubi ya ce: Ana ganin jama’ar da ta saba wa bai’ar Abubakar su ne digo na farkon na Shi’anci, wanda suka fi shahara a cikinsu, sun hada da: Salman Farisi, da Abuzar Gifari, da Mikdad dan As’wad, da Abbas dan Abdul Mudallib[4]. Bisa bayanin masu saba wa da bai’ar halifancin Abubakar ne, Dakta Ahmad Mahmud Subhi ya ce: Abubuwan da suka haifar da wannan sabani da suka sanya wasu barin bai’a ba zai yiwu a kafa dalili da su a kan cewa dukkaninsu Shi'a ba ne. Tayiwu abin da ya fada ya kasance gaskiya, amma masu tarihi sun karfafi cewa wadanda suka saba da bai’ar Abubakar cewa su Shi'a ne, kuma da sannu zamu yi nuni da hakan yayin bayanin game da hakan[5].
|