Halayen Manzon Allah (s.a.w)Tun da Allah yana son rabauta ne ga mutum shi ya sa halicce shi, don haka ne sai ya samar masa da hanya kamila da zai bi domin samun rabauta ta hanyar wasu amintattun bayi nasa da suke ma'asumai daga dukkan kuskure da mantuwa kuma tsarkaka daga dukkan aibobi da zunubai wadannan su ne annabawa da manzanni. Don haka ne: Annabi shi mutum ne da Allah ya yi masa wahayi ya zabe shi a cikin mutane kuma sun kasu gida biyu: Annabi dan sako shi ne wanda aka aiko domin ya tseratar da mutane daga duhu zuwa haske daga barna zuwa gaskiya daga camfi zuwa gaskiya daga jahilci zuwa ilmi. Annabi ba dan sako ba: shi ne wanda aka yi masa wahayi zuwa ga kansa kuma ba a umarce shi ya isar da sakon ga mutane ba. Yahudawa suna bin Annabi Musa (a.s) kiristoci kuma Annabi Isa (a.s) musulmi kuma Annabi Muhammad (s.a.w) da sauran annabawa duka. Sai dai musulunci ya shafe sauran addinai da suka rigaya, bai halatta ba ma'abotansu su wanzu a kansu, dole ne a Don haka yahudanci da kiristanci barna ne da aka shafe su, amma musulunci mai wanzuwa ne har zuwa ranar kiyama. Annabi Muhammad (s.a.w) shi ne karshen annabawa kuma addininsa shi ne musulunci mai shafe duk wani addini kuma shari'arsa zata wanzu har zuwa kiyama kuma ita kadai ce shari'ar da zata arzuta mutum da tabbatar masa da burinsa da amincinsa har zuwa karshen rayuwa duniya da lahira. Kamar yadda shi kadai ne mutum abin koyi ga dukkan duniya baki daya, dukkan mutanen duniya idan suna son alheri ga kawukansu to dole ne su bi tarfarkinsa su yi koyi da kyawawan halyensa (s.a.w) da kuma sanin sashen tarihinsa da ba makawa mu kawo wasu daga siffofinsa (s.a.w): Shi ne Muhammad dan Abdullah (s.a.w) kuma babarsa ita ce Aminatu 'yar Wahab. An haife shi a Makka ranar juma'a goma sha bakwai ga watan Rabi'ul awwal bayan bollolwar alfijir a shekarar giwa, a zamanin sarki mai adalci Kisra[2]. (wato idan an kwatanta shi da ire-irensa). An aiko Annabi Muhammad (s.a.w) da sako a 27 ga Rajab bayan yana dan shekara 40 yayin da Jibrilu (a.s) ya sauka gareshi daga wurin Allah (S.W.T) yana kogon Hira wanda yake dutse ne a Makka ya ce masa ka karanta kuma ya saukar masa da ayoyi biyar na surar Alaki[3]. Sai ya zo ya tsaya a
|