Halayen Manzon Allah (s.a.w)



Idan ya yi tafiya yana daukar madubi, da kwalli, da miswaki, da mataji, da kwalbar turare, da allura da zare, idan yana tafiya baya girman kai kuma ba ya nuna ragwanta ko kasala ko gajiyawa, idan an zo gangara sai ya yi tasbihi, idan kuwa an zo hawa sai ya kabbara, kuma duk inda ya sauka sai ya yi raka'a biyu tukun, sannan yana kin mutum ya yi tafiya shi kadai.

Manzon Allah (s.a.w) ya kasance mafi yawan tufafinsa farare ne, kuma yana son koren tufafi, sannan yana kwadaitar da mutane kan yin tsafta. Yana da zobuna da yake sanya su a hannun dama, sannan yana sanya kafar dama kafin hagu a sanya takalminsa, amma yana fara cire hagu kafin dama, yana da tufafi na musamman don sanya su ranar jumaأ¢â‚¬â„¢a.

Allah madakaki ya girmama shi da abubuwa, ya sanya yin salati gareshi tare da alayensa a matsayin wajibi addini da ya hau kan musulmi, sannan ya sanya biyayya gareshi da alayensa wajibi ne a kan dukkan mutane baki daya. Zancensa da na alayensa wasiyyansa dukkansa hikima ne kuma hujjar Allah ce kan talikai, kuma tafarkin tsira da shiriya ga duniya baki daya.

Domin hadafin manzon Allah (s.a.w) shi ne tsiratar da duniya gaba daya, don haka ne ya sanya soyayya da kauna su kasance jagorori a cikin alأ¢â‚¬â„¢umma baki daya, sannan ya sanya أ¢â‚¬ع©yanأ¢â‚¬â„¢uwantaka tsakanin musulmi a zamaninsa sai dai ban da gado da hani ya zo a kansa daga baya sai dai ga makusanta na jini. Da haka ne ya kafa wata alأ¢â‚¬â„¢umma mai karfi da ilimi, da son juna, wacce ta dauki nauyin yada wannan addini a duk fadin duniya baki daya.

Ya kasance ba ya tashi ko zama sai bisa ambaton Allah madaukaki, kuma yana zama inda ya samu sarari ne ba ya gwamatsar mutane, ya kasance yana daidaita kowa a bisa girmamawa. Majalisinsa wuri ne na jin kunya, da hakuri, da gaskiya , da amana, da kawaici, da girmama babba, da tausaya wa karami, da biyan bukatun mabukata.

Bai kasance mai kaushin hali ba, ya kasance mai sakin fuska, mai faraأ¢â‚¬â„¢a, mai taushin hali, ba ya aibatawa, ba ya zagi, ba ya alfahasha, kuma yana kau da kai daga abin da yake shaأ¢â‚¬â„¢awa, idan ya yi magana duk sai mutane su sunkuyar da kai kamar dai a kansu akwai tsuntsaye ne, sai dai idan ya yi shiru ne to sais u yi magana, kuma ba sa jayayya gunsa.

Da zai bar duniya ya bar wa alأ¢â‚¬â„¢ummarsa abubuwa biyu day a gaya musu idan sun yi riko das u ba zasu taba bata ba har abada, su ne; Littafin Allah da wasiyyansa alayensa tsarkaka goma sha biyu, hada da mai tsarki uwar alayensa matar wasiyyinsa na farko sayyida Zahara as, Allah ya sanya mu cikin cetonta. Ya wajabta son su kan kowa, da biyayya garesu da taimaka musu, da tsayawa idan suka tsayar da alأ¢â‚¬â„¢umma, sai dai alأ¢â‚¬â„¢umma ta yi watsi da wannan wasiyyar kamar yadda aka yi watsi da wasiyyar sauran annabawa

 

Rufewa:

Yayin da Allah ya halicci mutum yayin nufin alheri da rabautar duniya da ni'imar lahira da aljanna gareshi amma wannan duk ba ya samuwa sai idan mutum ya yi amfani da hankalinsa da kuma abin da ya dace da ruhinsa da jikinsa, wannan kuwa yana bukatara abin da zai dauke wadannan bukatu wadanda ba wanda zai iya samar da dukkan wannan sai mahaliccin mutum din da ya san shi kuma ya san bukatunsa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 next