Ra'ayoyin Jagoranci



Shi ma ra’ayi na biyun fonko ne kwatankwacin na farkon, kuma bai kafu bisa ilmi ba. Ra’ayin yana kama da irin hukuncin da mustashrikai suke yi wanda ya samo asali daga jahilci da kulli, da kuma ruhi irin na tsagwarar maddiyya wacce ba ta tafiya daidai da dabi’ar abin da yake gudana a musulunci. Mun ga irin wancan hukunci na rasar kunya da bashi da kanshin gaskiya wanda sashen mustashrikai suke yanke wa musulunci da Imaman

9  Ahlulbaiti (a.s). Ga abin da daya daga cikin su [3] ya fada kan Imam Hassan Mujtaba: cewa ya sai da halifanci ya karbi kudi! Ya gama rayuwarsa tare da turare da mata da walwala. Wani [4] kuma ya ce: Musulunci ya cirato al’umma daga matakin bauta zuwa na tsarin akda’(watau tsarinda talakawa basa mallakar filayen noma sai dai su yi aiki a filayen masu iko kana su raba amfanin)! Mahanga ta biyun tana tarayya da zantuttukan wadannan mustashrikai wajen biri-boko da garaje da kuma madogara ta maddiyya. Abin sha’awa a nan shi ne hujjojin da ma’abota ra‘ayi na biyu, watau ra’ayin ‘yan gurguzu, suka dogara da su ba komai ba ne face hukunce-hukuncen da ma’abota ra’ayin farko suka kirkiro!

SAHIHIYAR MAHANGA

MAHANGA TA UKU:-

Bari mu fara bayanin mahanga ta uku kan  lamarin Imam Sadik, ra’ayi da ko wani kaifin basira yana iya tsinkayar shi idan ya koma ga littafan riwaya. Wannan hukuncin ba ya takaita da rayuwar Imam Sadik kadai, a’a yana game dukkan Imaman Ahlulbaiti, bambancin kawai shi ne abin da aikin kowannensu ya kebanta da shi gwargwadon abin da yanayin zamani da wuri ya hukunta. Wannan sabawar kebantattun sifofin aikin ba ta cin karo da haduwar ruhin aiki da hakikaninsa ko kuma haduwar manufa da hanya.

Idan muna son fahimtar yanayin rayuwar Imamai ya wajaba da farko mu fahimci falsafar Imamanci. Tafiyar da aka san ta a mazhabar Ahlulbaiti da sunan Imamanci, wacce ginshikanta mutum goma sha biyu ne daya na bin daya kuma ta dauki kusan tsawon karni biyu da rabi, bisa hakika ci gaban aikin annabci ne. Shi annabi, Allah (s.w.t) yana aiko shi ne da wata sabuwar manhajar rayuwa, da sabuwar akida da wani sabon shirin alakokin dan Adam da kuma sako wanda aka dora masa, gwargwadon  shekarun da aka ba shi a wannan takaitacciyar rayuwa.

Wajibi ne kira ta ci gaba a bayan Annabi domin sakon ya cimma mafi daukakan matsayin da ake bukata wajen tabbatar da manufofinsa. Kazalika dole ne mutumin da ya fi kusaci da ma’abocin sakon ta dukkanin fuskoki ya dauki nauye-nauyen ci gaba da kira, domin sakon ya kai amintaccen matsayi, ya sami turke mai karfi, tabbatacce mara yankewa. Wannan aiki, babu shakka yana bukatar amintattun mutane. Wadannan sune Imamai, wasiyyan Annabi. Kuma dukkanin Imamai madaukaka kuma ma’abota sako suna da wasiyyai da halifofi. Ba za mu san nauyin al’amarin Imamai ba sai mun san na Annanbi, wanda Alkur,ani mai girma ya bayyana da cewa: “Hakika, lalle, mun aiko manzanninmu da hujjoji  bayyanannu, kuma muka saukar da littafi da sikeli tare da su domin mutane su tsayu da adalci……..” [5]  Wannan daya daga cikin ayoyi masu baiyana dalilin aiko annabawa da kuma nauyin da aka dora masu ne. An aiko su ne saboda gina wata sabuwar al’umma da tuge ginshikan fasadi da sanarwa kan aiwatar da sauyi ga jahiliyyar zamaninsu da kuma sake wa al’ummarsa fasali. Wannan shiri na kawo sauyi Imam Ali (a.s) ya bayyana shi a farkon karbar ragamar shugabancinsa da cewa :-. “ …..har sai na kasanku sun 10  zamo su ne a sama na samanku kuwa sun zamo su ne a kasa….”[6] Wannan aiki ne na  gina al’umma bisa asasin tauhidi da adalcin zamamtakewa da martaba  dan Adam da yanta shi da tabbatar da daidaiton hakkoki da dokoki a tsakanin jama’u da dai-daiku da yarfar da kangi da zalunci da boye kayan masarufi; da bude kofa ga karfi da kokarin dan Adam; da  kwadaitarwa kan neman ilmi, da ba da shi, da kwadaitarwa kan  tunani da sauransu. Shi aiki ne na kafa wata jama’a wacce a cikinta, ake habaka ilahirin hanyoyin daukakar dan Adam ta dukkanin muhimman fuskoki da kuma zaburar da shi don ya fuskanci tafiyan nan ta neman kamala a tsawon tarihinsa.

Saboda wannan nauyin ne Allah ya aiko annabawa.A matsayin Imamanci na ci gaba da daukar nauye-nauyen annabci, muna iya cewa yana daukar wadancan aiyuka. Da a ce Manzon Allah (s.a.w.a) ya rayu shekara 250 da wadanne ayyuka zai gabatar? Yanda ya aikata wajen kira haka nan  Imamai suka aikata. Manufar Imamanci ita ce ta annabci hanyar daya ce watau samar da al’umma ta musulunci adila da kokarin kare ingantaccer tafarkin musulunci. Sai dai abin da zamani yake hukuntawa yana bambanta, kuma gwargwadon wannan bambancin dabaru da solon aiki na sabawa. Annabi (s.a.w.a)da kansa ya yi aiki da wani salo a farkon kira wajen tabbatar da manufofinsa bayan an kai wani zango kuma ya yi amfani da wani salon  dabam.

Yayin da kirar take farkonta, tana kewaye da barazana da kalubale tana bukatar wani shiri na musamman  domin gudanar da aikin ida sako. Yayin da kuma ginshikan tsarin musulunci suka kafu, musulunci  ya sami kafuwa a Tsibirin Larabawa sai dabaru da salo suka sake.Tabbataccen al’amari na dindindin shi  ne madaukakiyar manufar da sakon ya sauko saboda ita. Shi ne kuma kokarin samar da al’ummar da a cikinta dan Adam yake iya tafiyarsa ta bidan kamala ta dukkanin fuskoki, a ciki ne kuma kwazo da karfin  da ke boye cikin halittar dan Adam za su bubbugo. A nan fa kariyar wannan al’umma da tsarinta na musulunci suke.

Imaman shi’a, kamar yanda Annabi ya yi, suna faskantar ainihin wannan manufar  ne watau kafa adalin tsari na musulunci mai wadannan  sifofi kuma bisa wannan tafarki. A dai dai lokacin da ake kafa wannan tsarin ana kuma ba da karfi wajen kariya da tabbatar da dogewarsa.



back 1 2 3 4 next