Ra'ayoyin JagoranciA zaton ma’abota wannan dubin Imam Sadik sam bai nuna wata damuwa kan wannan yanayi ba, a maimakon hakan ya gamsu da yin mukabala da ire-iren su Ibn Abi Awja, ya rufe masa baki da hujjoji ya kuma rinjaye shi duk da cewa ba zai ba da gaskiya ba. Wannan shi ne siffanta Imam Sadik da mazowa ra’ayin farko sukayi. MAHANGA TA BIYU:- Masu dauke da irin wannan dubin ba su yarda da imamancin Imam Sadik ba. Ita wannan mahanga tana ganin cewa ya nuna halin ko oho bisa zaluncin da yake aukawa al’umma. A zamamaninsa al’umma na kukan zaluncin yanayin zaman jama’a mai hawa-hawa da dagawar siyasa da babakere kan dukiyoyin jama’a [2] da hadarin da ya shafi rayuka da mutuncinsu. Dadin dadawa sarauta ta rinjayi hankula da rayuka da tunani da kuma zukatan mutane. Lamarin ya kai ga al’umma ta rasa mafi kankantan hakkokin bil Adama wanda ya hada da ikon zabe. A gefe guda kuma azzalumai suna ta wasa da makomar mutane yanda suka so, suna gina katafaran soraye kamar soron Al-hamra wanda ke makwabtaka da dubban kangwayen da matalautan al’umma ke zaune a ciki. Cikin wannan jama’ar da take dandana nau’i daban-daban na rashin adalci da danniya wai Imam Sadik ba abin da ya yi sai fuskantar bahasinsa da bincike da tarbiyyar dalibai, yana karkata dukkan kokarinsa kan samarda fukaha’u da masana ilmul kalam!! Hakika dukkan mahanga biyun nan sun bi son zuciya wajen hukunci kuma basu ginu kan wani tushe ba, basu kuma dogara kan wani dalili na gaskiya ba. Sai dai ra’ayin farko ya fi tsanani wajen bin son zuciya da zaluntar 8 Imam Sadik (a.s) tun da yake ya fito ne daga masu da’awar wai su shi’arsa ne kuma mabiyansa. A nan ban yi niyar daukan salon bahasin ilmin nan da aka saba bi wajen bincike-bincike, wanda a kan bijiro da dukkanin nassoshin da suka yi magana kan rayuwar Imam Sadik (a.s) sannan a auna wannan da wancan wajen matani da isnadi har a fitar da sakamako ba. Abin da nake nufi shi ne gabatar da nazari na uku wanda ya sha bam-bam da wadancan biyun. Sannan in auna shi da hujjojin da zan tsamo daga littattafan da suke hannunku’ domin, a matsayinku na alkalai ‘yan ba-ruwan mu, ku iya hango fuskar Imam ta hakika. Kafin in shiga cikin bahasin ya zama wajibi in yi nuni da cewa dukkanin nazariyyan na biyu basu dogara kan sahihin tushe abin amincewa ba. Kamar yanda na ambata, ra’ayin farko yana dogara kan wasu riwayoyi(na bayyana yanayin isnadinsu a kasa). Wadannan riwayoyi bisa dabi’a sun dace da bukatar masu neman hutu da gudun tsangwama suna fakewa da su a matsayin yankakken hujja.Lallai kam sun isa hujja ga raunanan zukata masu saukin girgizuwa! Wadannan riwayoyi sun sifanta Imam da cewa yana mai lallamin Mansur domin kare rayuwarsa duk da cewa yana iya magance yanayin da ya sami kansa ta hanyar hikima. Idan dai haka jagora yake, me zaton ka da mabiyi? Mun yi imani cewa yanayin nassin wanna riwaya ya wadatar wajen tabbatar da cewa kirkirarta aka yi. Ai Imam yana da damar tunkude sharrin Mansur ta wadansu hanyoyin daban kamar yanda amintattun riwayoyi suka nakalto abin da ya faru a wurare mayaiwata. Ashe babu dalilin da zai sa Imam ya koma wa lalama mara tushe ko yabon da ba na gaskiya ba, har ma ya baiwa Mansur halayen da ba shi da su da matsayin da bai cancance shi ba. Babu shakka matsayin imamanci ya daukaka sama da wannan, daukaka mai girma, darajarsa kuwa ta wuce irin wannan kaskanci ya gurbata ta. Ta bangaren isnadi kuwa, idan aka zurfafa bin diddigin masu ruwaya abubuwa da yawa za su baiyana a gare mu. Isnadin wasu daga cikinsu yana karewa ne kan Rabi’u Alhajib sarkin kofa.Sarkin kofan Mansur! Wannan kuwa akwai adali! Littattafai sun nuna cewa Rabi’u ya fi kowa kusanci da Mansur, ya fi kowa fada. Mansur ya yi masa waziri a shekara ta dari da hamsin da uku hijiraya watau shekaru biyar bayan wafatin Imam Sadik. Hakika Rab’u ya sami daukaka a matsayin ladan karairayin da ya kirkira ya kuma danganta su ga Imam. Irin wannan mutum wanda kusancinsa da alkawarinsa ga halifa ya tabbata ba abin mamaki ba ne ya kirkiri karairayi ya kuma jingina wa Imam Sadik lalama ko ya sake kalami mai zafi da Imam ya yi furuci da shi, ya mai da shi na kankan da kai da lallami. Wannan ba bakon abu ba ne wajen irin wannan bafaje, amma abin al’ajabin shi ne yanda mai hankali zai gaskata abokin sirrin halifa a kan abin da ya shafi abokan gabarsa, har ma a ce wai shi ma shi’a ne. Wannan kaulin shi ma wani yanki ne daga kule-kullen da kaskanci ne musabbabinsu.
|