Shi'anci Da Shi'a



c- Al'kanduzi Bahanife, Albalkhi, a littafinsa na Yanabi'ulmawadda tun wanda aka buga a Turkiyya lokacin halifancin usmaniyya.

d- Assayyid Muhamma Sadik Hasan Alkanuji Albukhari, alittafinsa na Al'iza'a limakana wamayakunu baina yadai assa'a.

Da sauran malamai magabata kamar: Dakta Mustapaha Rafi'i, alittafinsa islamuna, ya yi maganar haihuwarsa a ciki dalla-dalla.

21- Shi'a suna salla, suna azumi, suna zakka, suna bayar dahumusin dukiyarsu, suna yin hajji, a Makka, suna yin ayyukan umra da hajji na farkon a matsayin sauke wajibi, amma sama da hakan mustahabbi ne, suna umarni da kyakkyawa suna hani daga mummuna, suna bin masoyan Allah (S.W.T) da manzonsa (S.A.W), suna kin makiyansu, suna jihadi a tafarkin Allah ga dukkan mai yakarsu, ko kuma mai zagon kasa ga al'ummar musulmi gaba daya, suna aiwatar da dukkan ayyukansu daidai da hukuncin shari'a kamar: cinikayya, da haya, da aure, dasaki, da gado, da shayarwa, da hijabi, da tarbiyya.

Suna masu rikon wadannan hukunce-hukunce daga ijtihadi, damalamai suke yin sa daga littafin Allah (S.W.T) da sunnar manzonsa (S.A.W), dahankali, da haduwar malamai.

22-Shi'a suna ganin dukkan farilla ta kullum mai lokaciayyananne guda biyar ce wato: (asuba, azahar, la'asar, magariba, issah). Kuma suna ganin abin da ya fi shi ne a yi kowace sallah a lokacin da ya kebanta da ita wato lokuta guda biyar. Sai dai suna hada azahar da la'asar, da kuma magariba da issha, domin Manzo (S.A.W) ya hada shi ma ba tare da wani uzuri ba kamar na ruwan sama, ko rashin lafiya, ko safara, kamar yadda ya zo a littattafai kamar sahih Muslim, ba domin komai ba sai don ya saukaka kan al'ummarsa, wannan kuwa al'amari ne na yau da kullum a wannan zamani namu.

23- Shi'a suna kiran salla kamar sauran musulmi sai daibayan hayya alal falah, suna kara hayya ala khairil amal, kamar yadda yake a lokacin Manzo, sai dai umar dan khaddabi ya cire ta, domin yana ganin fadin hakan zai sanya musulmi su bar zuwa jihadi su shagaltu da salla don haka ya cire ta. (Kamar yadda malam Kushji al'ash'ari ya kawo a littafinsa: sharhin tajridul I'itikad, haka ma kindi a littafinsa, da muttaki: a kanzul ummal, dasauransu).

Kuma umar dan khaddabi ya kara assalatu khairun minannaumi azamaninsa abin da babu shi a asalin kiran salla, (Duba littattafan hadisai datarihi).

Shi'a suna ganin tunda ibada dole ta kasance kamar yadda maishari'a ya zo da ita, don haka ne duk wani abu dole ya kasance kamar yadda ya zo da shi, kuma duk wani kari kan hakan, kari ne kuma bidi'a ce da za a mayar da ita ga mai ita… don haka ne ya kasance ba sa yarda da dadi ko ragi a ibadasai abin da mai shari'a ya zo da shi, ba ra'ayi na waninsa ba.

Amma abin da Shi'a suke karawa na kiran salla da suke cewa:Ash'hadu anna aliyyan waliyyul Lah! Bayan sun kawo ash'hadu anna muhammadar rasulul Lah!, Wannan saboda wata ruwaya ce da suke da ita da take cewa babuwani waje da aka ambaci "Muhammadur rasululLah!" Ko kuma aka rubuta hakan a bakin kofar aljanna, sai an raba masa, "Aliyyun waliyyulLah". Wannan kuwa yana nuna Shi'a ba sa furuci da annabtar imam Ali (A.S) balle kuma batun ubangijintakarsa, kamar yadda masu yi musu kage da sharri sukefada. Wal'iyazu bilLah!.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next