Shi'anci Da Shi'a



Na biyu: Rarraba da sabani da jayayyatsakanin mazhabobi da kungiyoyin musulmi.

Don haka ne Shi'a a kodayaushe suke kirandukkan al'umma zuwa ga hadin kai da kuma neman yada soyayya da 'yan'uwantaka tsakanin dukkan al'umma, suna masu kuma girmama ijtihadodin malaman sauranmazhabobi da hukunce-hukuncensu.

A kan wannan ne malaman Shi'a sukatarbiyyantu tun karnonin farko na musulunci a kan ambaton ra'ayoyin malaman da ba Shi'a ba a littattafansu na fikihu, da tafsiri, da ilimin akida kamar littafin "khilafi' na Dusi a fikihu, da "Maj'ma'ul bayan" a tafsiri na Dabrasi, wanda manyan malaman azhar suka yabe shi. Ga kuma "Tajridul i'itikad" na Dusi a akida, amma malam Kushji ba'ash'are yayi masa sharhi.

37- malaman Shi'a suna ganin wajabcintattaunawa tsakanin malaman mazhabobi a fagen fikihu da akida da tarihi, da kuma fahimtar juna a fagagen mas'alolin musulmi na wannan zamani da kuma nisantar duk wani tuhuma da kuma kawar da zage-zage, har sai an samu damar samar da wani kusanci tsakanin al'ummar musulmi gaba daya, domin toshe wa makiya musulunci da musulmi hanyar tayar da rikici da gaba mai neman ganin bayan al'ummar musulmi gaba daya ba tare da ware wani bangare ba.

Don haka ne ma zamu ga cewa, Shi'a ba sakafirta wani daga ma'abota alkibla, koda kuwa mecece mazhabarsa, kuma ko mecece akidarsa, sai dai abin da dukkan musulmi suka hadu a kan ganin kafircinsa.

Shi'a ba sa gaba da wasu musulmi'yan'uwansu musulmi, ba sa yarda a hada kai da su wajen yi musu zagon kasa, ba sa yi musu makida, kuma suna girmama ra'ayoyin dukkan sauran mazhabobi, kuma suna ganin aikin duk wanda ya zama Shi'a a lokacin yana Sunna ya yi matukar ya yi daidai da wancan mazhabin nasa. Kamar aure, da saki, da salla, da hajji, dazakka, da azumi, da ciniki.

Don haka ba ya bukatar rama dukkanabubuwan da ya yi a da, da suka yi daidai da mazhabarsa ta da.

Shi'a suna rayuwa tare da 'yan'uwansumusulmi a kowane wuri kamar 'yan'uwansu na jini.

Amma Shi'a ba su yarda da sauranmazhabobin da turawan mulkin mallaka suka kafa ba, kamar baha'iyya, da babiyya, da kadiyaniyya, da sauransu, kuma suna saba musu matuka, kuma suna haramtakarkata zuwa garesu.

Shi'a ba kodayaushe suke yin takiyya ba,takiyya tana nufin boye mazhabarka ko ra'ayinka, wannan kuwa al'amari ne na shari'a da nassin Kur'ani ya zo da shi, kuma dukkan mazhabobi suna amfani da shi a wasu yanayoyi na rikici da cutuwa. Kuma abubuwan da suke jawo hakan gudabiyu ne:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next