Shi'anci Da Shi'a



Makaloli Game Da Shi'anci Da Shi'a A Duniya

Wallafar: Sheikh Jafar Al'hadi

Fassarar: Hafiz Muhammad Sa’id

“KawaiAllah yana son ya tafiyar da dauda daga gareku ne Ahlul Baiti kuma ya tsarkake ku tsarkakewa[1].

“Lallai ni mai bar mukunauyaya biyu ne; Littafin Allah da Ahlin gidana, ba zaku taba bata ba bayanahar abada matukar kun yi riko da su.[1].

BukatarSanayya

Muka sanya ku jama'u da kabilu domin ku sanjuna…

Musulunci ya zo alhalin jama'u suna rarrabe masukyamar juna, masu fada da yake-yake, amma sai ya gaggauta domin warware wannan ya mayar da sanayya mahallin kiyayya da kyama, ya sanya taimakekeniya mahallin jayayya da husuma, ya sanya sadarwa tsakanin juna a mahallin yankewa, wannan kuwa duk da albarkacin koyarwa musulunci ta tauhidi da kadaita Allah ne. sai a sakamkon haka aka samu bayyanar wata al'umma mai girma da wayewa da cigaba mai girma, kamar yadda ta kare al'ummunta daga zaluncin dukkan wani azzalumi mai danniya, wannan al'umma ta zamanto mai kwarjini da ban tsoro a idanun duk waniazzalumi mai dagawa.

Wannan kuwa duk bai samu ba sai da albarkacin hadinkai da sadarwa tsakanin jama'u wadanda suka taru karkashin inuwar musulunci guda daya, duk da kuwa nau'o'in jinsinsu, da sabanin ijtihadodinsu, da yawaitar kabilunsu da sabanin al'adunsu, don haduwa a asasi da asali da farillai da wajibai ya ishesu, don haka hadin kai karfi ne, amma rarraba rauni ce.

Al'amarin ya ci gba da haka har sai da aka sakemayar da wanna soyayya ta koma kiyayya, fahimtar juna ta koma kyamar juna, sashensu suka kafirta sashe, aka yi doke-doke tsakanin juna.

 Sai wannan girma da izza suka kawu dagacikinsu, azzalumai suka sake yi musu hawan kawara, suka kutsa cikin gidajensu kwararo-kwararo, suka daidaice, suka warwatse, aka wawashe arzikinsu, aka wulakanta huruminsu, aka keta mutuncinsu karkashin fajirai, suka rika yin kasa-kasakullum, da rushewa da take bin su faduwa bayan faduwa.

Da shan kashi a hannu a Andulus, da bukhara, dasamrakand, da Daskand, da Bagdad, a da can, da kuma a yau a palasdin daAfganistan.

Idan ta yi kira ba a amsa mata, idan ta nemitaimkao ba a taimaka mata, yaya kuwa haka zata faru alhalin cutarta wani abu nedaban, maganinta wani abu daban ake ba ta.

Alhalin Allah ba zai yarda ba, sai dai al'amurasu tafi daidai gwargwadon sababinsu, kuma karshen wannan al'umma ba zai gyaru ba sai da abin da farkonta ya gyaru da shi.



1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next