Hukuncin Dukiya



Don haka duk sa'adda aka gano mai ita a koda yaushe ne kuma komai tsawon lokaci, ya zama dole a yi mata hukuncin dukiyar da aka san adadinta kuma aka san mai ita, don haka ya zama wajibi ne a biya shi.

 

4- Jahiltar Mai Dukiya Da Jahiltar Adadi

Dukiyar da ba a san mai ita ba, ba a san adadinta ba, sai a bincika game da shi, idan ba a same shi ba, alhalin wannan dukyar tana cakude da dukiyar wanda take hannunsa.

Wannan dukiyar idan ta yadu a cikin dukiyarsa sai fitar da humusin dukiyarsa domin tsarkake ta.

Malamai sun yi sabani kan cewa shin dukiyar gwamnati wato wacce take ta al'umma ce dukiyar da aka jahilci mai ita ce, ko kuma dukiyar da aka san mai ita ce, sai wadannan hukunce-hukuncen su bi ta.

Idan malami ya yi ijtihadi a kan cewa dukiyar gwamnati an san mai ita, to a nan babu wani ikon dauka a yi amfani da ita, amma idan malami yana ganin ta a matsayin dukiyar da aka jahilci mai ita, to a nan yana nufin ya halatta mutum ya yi tasarrufi da ita.

Sai dai hatta malamanmu da suka tafi a kan ra'ayin cewa dukiyar gwamnati tana da hukuncin wanda ba a san mai ita ba ne, su ma sun tafi a kan cewa duk wani tasarrufi da ita wannan dukiya dole ne ya kasance da izinin mujtahidin mabiyi.

Sannan kuma ba zai yiwu ya yi wani abu na gaban kansa da irin wannan dukiyar ba sai da izinin wanda yake biyayya gareshi na daga malamai.

Don haka babu wani abu da babu tsari gareshi a cikin shari’a, da shari’a zata yardarwa kowane mutum ya dauki dukiya koda kuwa babu izini gareshi a bisa tsarin kasa da an zo da barna mai girma, da an koma wa rashin tsari wanda zai kai ga arzuta wasu, da talaucin wasu, da wasu sun samu damar fakewa da hakan domin barnar dukiyar al’umma.

Sai dai wannan hukuncin yana kebantar wanda aka ba wa fatawar yin hakan shi ma bisa wasu la’akari da shari’a ta gindaya su. Don haka sai kowa ya koma wa madogararsa domin neman cikakken bayani kan wannan lamari mai hatsari, domin ya kare kansa daga dora wa kansa hakkokin al’umma a kansa, kuma ya samu tsira wurin Ubangijinsa.

Cibiyar Al’adun Musulunci

Hafiz Muhammad Sa’id

Hfazah@yahoo.com

www.hikima.org

Tuesday, April 13, 2010



back 1 2 3 4