Hukuncin DukiyaBa don wannan hukuncin ba da tsarin al'umma ya yamutse, da an samu halatta dukiyoyin al'umma bisa barna, da duniya ba ta samu nutsuwa ba. 2- Sanin Mai Dukiya da Jahiltar Adadi Dukiyar da aka san mai ita, ba a san adadinta ba kuwa, ita wannan dukiyar sai a yi sulhu bisa wani adadi da zai yardar da juna. A bisa yanayin wannan dukiya tun da an san mai ita, to a shar'ance dole ne ta koma hannunsa, sai dai zai kasance an samu fuskantar matsala guda daya ta cewar ba a san adadin wannan dukiya ba. Kamar dai wanda ya ba wa wani mutum rance ne amma sai suka manta da adadinta, to a nan sai su yi sulhu bisa wani adadi na dukiya da zamu samu yarda da nutsuwa a kai. 3- Jahiltar Mai Dukiya Da Sanin Adadi Dukiyar da ba a san mai ita ba, amma an san adadinta tana da hukuncin yin sadaka da ita ga mai ita. Sai dai wannan yin sadakar da ita ba ya nufin idan mai ita ya zo wata rana ko aka gano shi cewa ba za a ba shi dukiyarsa ba.
|