Kimar Mutum



Wannan mutumin ya cika maras kima, kuma ya kai matukar makurar kaskanci, yayin da ya dauki alherin da wasu suka yi masa abin da yi wa dariya da isgili!. Lallai maganar masu hikima ta gaskata yayin da suke cewa: Idan ka girmama mai karimci sai ka mallake shi, amma idan ka girmama kaskantacce sai ya yi dagawa. Domin babu wani mai fahimtar alheri sai ma’abocin alheri, amma kaskantaccen mutum wanda bai san alheri ba, idan ka yi masa alheri sai ya yi dagawa, ko ya ga wani wayo ne ya ba shi hakan. Misalin Karuna babbban misali ne a wannan fage yayin da yake cewa: “Ai duk sanina (dubarata) ne suka ba ni wannan dukiya...” (Kasas: 78).

Idan mutum ya daukaka yana da matukar girma da daraja, amma idan ya fita daga kimar nau’insa, sai ya koma mafi kaskantar halittun duniya. A ilimin Mantik ana yin bayanin cewa; mutum shi ne mai rai mai hankali, sai ga mutum a yau ya komai mai rai mai farautar dan’uwansa mutum. Ba zaka ji komai ba a duniya sai kisa, da fashi, da yaudara, da zambo, da gaba, da kiyayya, da fushi, da rashin zaman lafiya, da rashin tsaro, da talauci, da cututtuka, da makamantansu. A Jiya ne ma wani yake bugo mini waya cewa; Ai ‘yan fashi sun tare hanyar su Tsohon Gwamna Abubakar Rimi, sai ya samu bugawar zuciya sai ya mutu kafin a karasa asibiti!.

Kuma haka nan kissar take ga dubunnai da miliyoyin mutanen da suke rayuwa a duniya, a kullum firgici, da tsoro sai sun yi kisa bisa dalilai iri-iri. Kamar yadda a kullum Allah ne kawai ya san yawan matan da ake zubarwa mutucinsu ta hanyoyi mabambanta mafi muninsu shi ne fade!.

Wannan kuwa ita ce makomar dan Adam matukar ya yi nisa da sakon Allah, a koda yaushe dan Adam ya yi nisa daga tafarkin haske, to zai zurfafa cikin duhun faganniya kenan.

Don me ya sanya mutum ba zai yi tunanin meye matsalar ba! Don me ba zai koma cikin hankalinsa ya yi tunani ba?! Shin muna tsammanin haka Allah madaukaki yake son duniya ta kasance ne?! Shin muna tsammanin cewa Allah bai yi duniya don rahama ba, ya yi ta ne don wahala?! Shin muna tunanin cewa wadannan abubuwan da suke faruwa ba su da dalili ne?! kuma shin mun sanya tunani domin ganin mun kama hanyar warwara?!

Ganin halin da duniya take ciki ya sanya mutanenta sun yanke kauna daga samun gyara, wannan kuwa shi ne ya fi komai muni, domin ba masu yanke kauna sai mutane batattu. Idan mutane suka yanke kauna to tabbas sun kauce hanyar Allah ne, amma muminai suna ganin hanyar gyara a wartsake, sai dai duniya ba ta sallama wa maganarsu, don haka dole ne wannan faganniya da dimuwa ta ci gaba.

Amma Allah madaukaki ya yanke duk wani uzuri ga dan Adam, kuma ya girmama shi, ya shiryar da shi duk wani tafarki, ya yi masa duk wata falala yana mai cewa: “Hakika mun girmama 'yan Adam, muka dauke su a tudu da kogi, muka arzuta su daga dadada, kuma muka fifita su a kan mafi yawan abubuwan da muka halitta fifitawa. (Isra'i: 70)

Sannan ya fifita shi a kan duk wata  halitta kowace iri ce, ya sanya shi mai matsakaicin hali da idan ya ga dama sai ya fi mala’ika, idan kuwa ya ga wata damar sai ya fi duk wata halitta kaskanci. Kuma wannan ruwayar tana nuna mana haka a sarari yayin da take cewa: An karbo daga Imam Sadik (a.s): -yayin da Abdullahi dan Sinan ya tambaye shi Mala'iku ne suka fi ko 'ya'yan Adam?- sai ya ce: "Amirul Muminin Ali dan Abu Dalib ya ce: Ubangiji madaukaki ya sanya wa mala'iku hankali babu sha'awa, ya sanya wa dabbobi sha'awa babu hankali, sai ya sanya wa 'dan Adam duka biyun, to duk wanda hankalinsa ya rinjayi sha'awarsa to shi ya fi mala'ika, kuma duk wanda sha'awarsa ta yi galaba kan hankalinsa to ya fi dabbobi kaskanta. (Biharul Anwar: 60/299/5).

Idan mutum ya samu kamala yana iya zarcewa ya tafi babu iyaka ga kamalarsa domin daga Allah take wanda ba shi da iyaka. Yana iya kasancewa shi kadai ya fi dukkan mutane da sauran halittu daraja kamar yadda yake ga Annabi (s.a.w) da alayensa (a.s). Don haka ne zamu ga wata ruwayar tana nuni da hakan tana mai cewa: Daga Annabi (s.a.w): "Babu abin da ya fi dubunsa daga irinsa sai mutum". (Kanzul Ummal: 34615). Don haka ne zaka ga mutum daya amma ya fi miliyoyin mutane daraja.

Babbar ni’imar da Allah madaukaki ya yi wa mutane shi ne ta rashin toshe musu kofar kamala matukar suna son su samu kamalar. Kuma wannan kofa har su mutu ba a toshe ta, sannan kuma akwai wasu kofofin da ba su da iyaka da suke a bude har bayan mutuwa!.



back 1 2 3 4 next