Kimar MutumDa sunan Allah madaukaki Mutum halitta ce mai girma daga cikin halittun Allah madaukaki wanda ya girmama shi fiye da kowace halitta, sai dai wannan halitta mai girma da kima mai wuyar sha’ani yana iya kaiwa matakin da ya fi kowace halitta kamar mala’iku madaukaka, kamar yadda yana iya kaiwa mafi munin halitta da yake kasan darajar alade, kuma wannan lamari ya sanya mutum mai wuyar sha’ani, murdadde. Daya daga cikin mafi girman ni’imar da Allah ya yi wa mutum ita ce bude masa hanyoyi biyu na kamala da na kaskanta. Madaukaki yana cewa: “Mu mun nuna masa tafarki ko ya kasance mai yawan godewa ko mai yawan kafircewaâ€. (Insan: 3). Da fadinsa: “Mun shiryar da shi tafarki biyu†(Balad: 10). Domin mutum ya samu daukaka da kamalar dan’adamtaka yana bukatar ya samar da alaka uku ne wacce kowacce daga cikin tana da dokoki da hanyoyi da zai iya kyautatawa. Wadannan alakokin mafi muhimmanci da kima da daraja da girma ita ce alaka da mahalicci, sannan sai alaka da mutum, sai kuma alaka da sauran halittu. Sannan wadannan alakokin suna shiga cikin juna ne, ba su kasance hannun riga da junansu ba, don haka kyautata kowacce daga cikinsu tana da alaka da kyautata sauran. Idan mutum ya kyautata alakarsa da Allah madaukaki to yana nufin ya kyautata duka ukun ne. Sannan a wannan rubutun namu zamu karfafi bayani kan alakar mutum da dan’uwansa mutum ne. Idan mun duba alakar mutum da dan’uwansa mutum zamu ga mutane sun kasu gida biyu; imma dai suna da kimanta jinsinsu na mutane ko suna kaskantar da su. A ilmance an sanya wannan lamarin a matsayin ma’aunin gane mutum mai kima da daraja, domin idan mutum mai kima ne sai ya kimanta dan Adam domin kansa yake nunawa ta yadda kimarsa takan sanya shi jin sauran mutane suna da kima, amma idan kaskantacce ne sai ya yi tsammanin kowa ma haka yake. Kuma haka lamarin yakan juya ga wanda aka girmama idan mai kima da daraja ne sai ya girmama ka, amma idan mai kaskanci ne sai ya yi takama. Masu hikima suna cewa: “Idan ka girmama mai daraja sai ka mallake shi, idan kuwa ka girmama kaskantacce sai ya yi dagawa da girman kai†(Al’mu’utamaratus Salas: Husain Shakiri/ s 147). Kamalar Annabi (s.a.w) da imamai magadansa masu daraja ce ta sanya mu gane cewa su ne masu mafi daukakar darajoji a cikin kowane fage na ilimi da sani, da kyautata alaka da mahaliccinsu da sauran bayi mutane, da kuma sauran halittu, fiye da kowane mahaluki.
|