Sakon Annabi Muhammad (s.a.w)A wata ruwayar Sheikh Mufid ya karbo daga majalisinsa da sanadin da muka ambata daga Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: Manzon Allah (s.a.w) ya hau kan mimbari sai fuskarsa ta canja kuma launi ya juya sannan sai ya fuskanto da fuskarsa ya ce: "Ya ku jama'ar musulmi! Ni an aiko ni ne kusa da alkiyama … -har inda yake cewa- ya ku mutane wanda ya bar dukiya to ta iyalinsa ce da magadansa, amma wanda ya bar wani nauyi ko rashi to yana kaina a zo gareni"[4]. Haka nan ya karbo daga Abu Abdullahi (a.s) ya ce: Wanda yake da wata dukiya kan wani mutum da ya karba kuma bai ciyar da ita a barna ko sabo ba sai ya kasa biya, to wanda yake binsa dole ne ya jira shi har sai Allah ya arzuta shi sai ya biya shi, idan kuwa akwai jagora mai adalci to yana kansa ne ya biya masa bashinsa, saboda fadin Manzon Allah (s.a.w) cewa: "Duk wanda ya bar dukiya to ta magadansa ce, kuma wanda ya bar bashi ko wani rashi to yana kaina ku zo gareni, don haka duk abin da yake kan Annabi (s.a.w), yana kan jagora. (Mustadrikul wasa'il, mujalladi 4, shafi: 492). Da wdannan dokokin da ire-irensu masu yawa da ba mu kawo su ba ne Musulunci ya sanya talauci ya kawu daga dukkan daular da take kusan fadin kwata na duniya gaba daya a wancan zamanin. Talauci ya kawu ta yadda kusan idan ka ga mai roko to zai kasance abin mamaki, musulunci ba ya son zama cikin kaskancin rokon mutane, don haka ne ya kawar da talauci, ya sanya dokokin lamunin rayuwar al’umma. Duba mamakin da Imam Ali ya yi yayin da ya ga wani yana bara a kwararon birinin Kufa. Hurrul amuli ya ambaci cewa: Imam Ali (a.s) yana tafiya a cikin lungunan garin Kufa wata rana, sai ya ga wani mutum yana rokon mutane, sai ya yi mamaki sosai, sai ya juya da shi da wadanda suke tare da shi suna tambayarsa Mene ne haka? Sai ya ce: Ni tsoho ne kuma kirista na tsufa ba na iya aiki kuma ba ni da wata dukiya da zan rayu da ita, sai na shiga bara. Sai Imam Ali (a.s) ya yi fushi ya ce: Kun sanya shi aiki yana saurayi sai da ya tsufa zaku bar shi?! Sai ya yi umarni a sanya wa wannan kirista wani abu na albashi daga Baitul-mali da zai rika rayuwa da shi (Wasa'ilus Shi'a). Wanan kissa tana nuna cewa; Talauci ya kawu gaba daya har sai da ya kasance ba shi da wani mahalli a daular musulunci. Hatta Imam Ali (a.s) da ya ga talaka guda daya mai bara kuma ba ma musulmi ba sai da ya yi mamakinsa, ya gan shi wani abu bare da bai dace da al'ummar musulmi ba. Sannan ya yi umarni da a sanya masa albashi da zai rayu da shi tare da cewa shi kirista ne da ba ya riko da musulunci, domin kada a samu talaka a kasar musulmi ko da kuwa mutum daya ne. Kuma domin duniya ta san abin da musulmi suke a kai na yaki da talauci: da cewa kuma hukumar musulunci ita ce take yaki da talauci ta kuma daukaka matsayin talakawa ba kawai musulmi ba, har da wasunsu matukar suna karkashin daular. Haka nan musulunci ya dauki dan Adam da kima matuka ko da kuwa bai musulunta ba, sai dai duk wanda ya taba musulmi ya kashe su to shi kadai ne musulunci ya yarda musulmi su taba, don haka ne zamu ga a rayuwar Manzon Allah (s.a.w) bai taba kai hari kan mutanen da ba su suka fara kai masa hari ba. Kuma idan mutanen wani gari suka kai masa hari to bai taba yakar wasunsu na wani garin daban ba ko da kuwa addininsu daya ne, sai dai ya rama kan wadannan dai da suka kai masa hari kawai. Duk da a rayuwar musulunci an samu yakoki masu yawa a Madina kuma dukkanninsu sun zama domin kare kai ne daga makiya mushrikai da yahudawa da kiristoci da suke kai hari kan musulmi, kuma Annabi a kowne lokaci yana zabar bangaren sulhu da zaman lafiya ne da rangwame. Don haka ne ma adadin wadanda ake kashe wa bangarorin biyu ba su da yawa a dukkan yakokinsa tamanin da wani abu. Wadanda aka kashe na musulmi da kafirai duka ba su kai sama da dubu daya da dari hudu ba. (Littafin Tafarkin Rabauta: Fasalin; Aiko Annabi Mai Daraja (s.a.w). Musulunci bai taba yarda da zaluntar wani mutum ko wani mai rai ba, kai hatta da barnar abinci da lalata wuri da lalata kasa ya hana balle azabtar da dan Adam ko kashe shi, ya kuma sanya kalma mai dadi da zaka gaya wa dan'uwanka mutum ya yi farin ciki a matsayin sadaka. Don haka ne ya soki mai lalata kayan gona da dabbobi, ya kira shi mai yada fasadi da barna, balle kuma mai isar da cutarwa ga mutum. Saboda haka ne ma muka samu dukkan matsalolin da muke ciki a yau musamman a kasashenmu sun taso daga rashin fahimtar musulunci ne, sai dan Adam ya kasance ba shi da wata kima. Mun rasa ilimi ta yadda yawancin mutanenmu suna rayuwa a matsayin masu karancin ilimi ko ma ba su da shi saboda kawai yarenmu ba a yarda ya zama yaren ilimi ba, sai wannan karancin ilimin da rashin lamunin rayuwar suka haifar mana da rashin ganin kimar dan Adam. Muna iya ganin yadda aka kashe mutane babu imani, ko tausayi, ko hankali, kamar yadda Aljazira ta nuna a rikicin da ya faru a Maiduguri, ta yadda aka kashe mutanen da su ba “Yan boko haram†ba ne, (kai ko da ma su ne ya kamata a kai su kotu domin doka ta zartar musu da hukuncin da ya dace ne). Har ma mai harbin ana gaya masa kada ya lalata bulet, kuma ya bar kai domin ana bukatar hular, wannan lamari mai ban takaici ya yi nuni da cewa; hatta da alburushi da hula sun fi dan Adam kima. Sai ga ma’aikacin da aka dauka aiki domin ya kare al’umma yana harbe su ba su ji ba su gani ba, ana biyansa albashi da kudin al’umma domin ya kare ta, amma sai ga shi hatta da raunanan mutane kamar guragu yana kamowa yana harbewa. Kuma idan dai ba a dauki mataki kan wadanda suka yi wannan ba, to tabbas wata rana shi wanda ya sanya su yin hakan zasu yi wa danginsa ko shi ma ta fada kansa. Domin idan rashin hankali, da rashin imani, da kekashewar zuciya, da rashin tausayi, da rashin doka, suka yi jagoranci, to babu makawa zasu shafi kowane mutum ne. Idan rashin tsoron Allah da tunawa da cewa za a mutu a koma ga Allah ya yi hisabin dukkan abin da muka yi ya mutu murus, to sakamakon da za a samu kenan.
|