Sakon Annabi Muhammad (s.a.w)Da matakin: "Abd" ne ya taka matakin "Hamd" domin karshen matakin "Abd" zai kai ga matakin "Hamd" sai Allah ya kasance Hameed shi kuwa Muhammad. Yayin da ya taka matakin "Hamd" sai ya siffantu da rahamar Ubangiji, don haka ne bayan gode wa Allah sai kirarin rahamarsa kamar yadda ya zo a surar Fatiha. Sai ya gadar da wannan rahamar ga wasiyyai, da wannan ne sayyidi Ali (a.s) yake cewa: "Ni bawa ne daga bayin Muhammad" (Shifa'ussudu: Mirza Abul Fadhl Tehrani; 449). Sai wadancan haskaka goma sha biyu da 'yarsa Zahara (a.s) suka kasance feshi daga rahamar Allah ta hannun Muhammad (s.a.w) bawansa, Rininsu da saninsu na Allah ne. (Shifa'ussudu: Mirza Abul Fadhl Tehrani; 449). “Rinin Allah waye ya fi Allah iya rini, kuma mu masu bauta ne gareshi†(Bakara: 138). Sai Allah ya runa su da shiriyarsa da rahamarsa, sai suka runa mu da shiriyar da Allah ya yi musu, don haka ne Muhammad (s.a.w) ya kasance rahamar Allah ga talikai baki daya, a bayansa kuma Littafin Allah da Alayensa (a.s). Sai aka wajabta salati gareshi tare da wadannan Alayen nasa goma sha uku, sai aka yi masa ni’imomi da babu wanda ya same su. Mataki ne na “Hamdâ€, da wajabcin yi masa salati. Da wasu ni’imomi kuma da babu mai samun su sai ya roka kamar yadda aka yalwata masa kirjinsa, aka sanya masa Ali dan’uwansa wasiyyinsa mai karfafarsa... “Shin ba mu yalwata maka kirjinka ba†(Sharh: 1). Amma Annabi daga Ulul azm kamar Musa (a.s) bai isa ya samu ba sai ya roka. “Ya ce: Allah ka yalwata kirjina... ka sanya mini mataimaki daga ahlina, dan’uwana Harun…†(Taha: 25 - 35). Sakon Manzo (s.a.w) Babu wani addini da ya zo da rahama ga al’umma fiye da wannan addini na karshe, domin wanda aka aiko da shi yana dauke da rahamar Allah (s.w.t) tare da shi. Don haka ne ma “... Ba mu aiko ka ba sai rahama ga talikai...†(Anbiya: 107). Da wannan ne zamu ga addinin nan madaukaki na musulunci ya zo da lamunin rayuwar dukkan dan Adam wacce ba ta kebanta da musulmi ba. Akwai ruwayoyi masu yawa da suka zo game da daukar nauyin al'amuran al'umma da zamu kawo wasu kamar hakan: Daga Abu Abdullahi (a.s) ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Ni ne na fi cancanta da kowane mumini fiye da kansa kuma Ali (a.s) shi ne ya fi cancanta da shi bayana". Sai aka ce da shi Imam Ja'afar Sadik me wannan yake nufi? Sai ya ce: Fadin Annabi (s.a.w) wanda ya bar bashi ko kaya to suna kaina, wanda kuwa ya bar dukiya to ta magadansa ce"(Tafsiri Nurus sakalain: mujalladi 4, shafi: 240). A wata ruwaya ta Ali bn Ibrahim ya kawo a tafsirinsa daga Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "Babu wani wanda yake bin bashi da zai tafi da wanda yake bi bashi wajen wani jagora na musulmi kuma ta bayyana ga wannan shugaban cewa ba shi da shi, to sai shi wannan talakan marashi ya kubuta daga bashinsa kuma bashinsa ya koma kan jagoran musulmi da zai biya daga abin da yake hannunsa na dukiyar musulmi"[2]. Bayan Imam Sadik ya fadi wannan hadisi daga Manzon Allah (s.a.w) sai ya ce: "Babu wani dalili da ya sanya mafi yawan yahudawa musulunta sai bayan wannan magana ta Annabi (s.a.w), kuma sun yi imani da su da iyalansu"[3].
|