Sakon Annabi Muhammad (s.a.w)



 

Da SunanSa Madaukaki

Amincin Allah ya tabbata ga Annabi da Alayensa

 

"Ba mu aiko ka ba sai don rahama ga talikai" (Anbiya: 107). Rahamar Allah ita ce abu na farko da ya bayyana ga bayinsa bayan bayyanar sunansa Allahu, don haka ne ma rahamarsa ta yalwaci kowane abu. Rahamar Allah a nan ta mamaye dukkan janibin halitta a samuwarta, da kuma tsarin rayuwarta da aka fi sani da Shari'a.

Shi rahama ne a Shari'a da ma'anarta mai fadi da ta shafi siyasa, tattalin arziki, zaman tare, tsaron al'umma, yalwar al'umma[1], rayuwar auratayya, hakkokin yara da na mata, da raunanan mutane, hukunce-hukuncen ibadoji da mu'amaloli, kawar da talauci da fatara daga cikin al'umma, ilmantar da al'umma gaba daya ta yadda ba za a samu jahili ko da daya ba, samar da mazauni da matsuguni ga kowane mutum. Rahama ce ga dukkan talikai da tsarin da zai samar da adalci a cikin al'ummu duk duniya baki daya, da ta yalwaci kowane abu, balle kuma dan Adam mai kima da daraja. Don haka ne yayin da duniya ta kasance cikin duhu sai garinta ya waye da wanda Isa dan Maryam (a.s) ya yi wasiyya da zuwansa Muhammad (s.a.w).

Rahamar ba ta tafi ba don wafatinsa, domin rahama ce mai fadi da ta yalwaci kowane abu har alkiyama ta tashi, don haka ne ma ya zaba mata mahalli har goma sha biyu da zasu kasance bayyanar rahamar bayan wucewarsa. Ita siffa ce mafificiya ga Manzon Allah, Suna ne da Allah ya tsaga shi daga gareshi ya yafa masa shi, don haka ne ya zamanto rahama ga dukkan talikai da rahmaniyyarsa, rahama ga muminai da rahimiyyarsa da ta tsattsago daga rahamaniyyarsa.

Sai ya kasance yana da fifikon da babu wani mahaluki da ya taka shi, wannan matakin shi ne matakin "Hamd" wanda alaminsa shi ne "Tutar Hamd", sai ya sanya mai rikon wannan tutar shi ne wasiyyinsa Ali (a.s), yana cewa da shi: "Kai ne mai rikon tutata duniya da lahira". (Duba Kanzul Ummal na Muttaki Hindi, Bahanife: J 13, Hadisi: 36476). Sai Manzon Allah ya taka matsayin "Hamd", Alinsa kuwa yana kan "Tutar Hamd", don ya yi nuni da cewa ga kofarsa nan da duk wani da ya wuce ba ta nan ba, to ba zai iso gunsa ba.

Kasancewarsa rahamar Allah ga bayi, kuma wanda ya taka mataki mafi girma na "Hamd=Godiya", don ya kasance mai yawan godiya ga Ubangijinsa, ibadarsa ba don tsoron wuta ko kwadayin aljanna ba, wannan ita ce ibadar bayi da masu kwadayi, amma ibadarsa ta kasance don godiya ce ga Allah. Sai ga tsokar jikinsa Zahara (a.s) take nanata cewa da Ubangiji ya azabtar da ita a wutarsa, da ta riki tauhidinta a hannu.

Imam Ali (a.s) kuwa wanda yake rike masa "Liwa'ul Hamd = Tutar Godiya" yana munajati da Allah yana cewa: Kuma wallahi! da ka sanya ni a cikin azaba tare da makiyanka, ka hada ni a wuta a tsakanin wadanda bala'inka ya fada wa, na rantse da girmanka ya madogarata jagorana, ina mai rantsuwa mai gaskatawa, matukar ka bar ni ina magana, to zan daga murya zuwa gareka tsakaninsu -'yan wuta- da muryar masu buri, kuma wallahi sai na kira ka ina kake ya masoyin muminai, ya matukar burin masana, ya mai taimakon masu neman taimako, ya masoyin zukatan masu gaskiya, ya Ubangijin talikai! (Muhasabutun Nafs: Kaf'ami; S: 187).



1 2 3 4 next