Tattaunawa Ta Biyar



Kuma a nan "lazim akali" ba hujja ba ne haka ma Urfi. Domin yana karo da nassi.

 Waye Abdurrazak da kake cewa bai inganta Hadisuddar ba? Bin ibrahim khurasani ko bin hammam yamani, ko aljilani ko waye… ba mutum daya ba ne a ilimin ruwayoyi mai wannan suna sai ka kawo inda ya ture ta, kuma bisa wacce hujja ce. Sannan kuma ka sani wannan hadisi bai kebanta da Mustadrak ba! Amma hadisin manzila ya zo a wurare masu yawa kamar haka:

Na daya: Lokacin â€کyan’uwantaka da ya sanya wa kowa dan’uwa ban da Ali (a.s) sai ya gaya wa Imam Ali (a.s) wannan maganar. Kuma Suyudi a Durrul Mansur ya ruwaito shi a tafsirin ayar nan ta “Allah ne yake zabar manzanninsa daga mala’iku kuma daga mutane…â€‌ daga Bagawi da Bawardi da Ibn Kani’ da Tabrani da Ibn Asakir.

Da manakibu Ali gun Ahmad bn hanbal, da manakibul ashara, da kanzul ummal a manakibu Ali (a.s). wannan fa ka duba duk malaman Sunna ne.

Na biyu: A hadisuddar da ya gabata a cikin muhawarorinmu.

Na uku: A hudubar ranar Gadir ya ambace shi da kalmar wazirinsa.

Na hudu: A al’amarin toshe dukkan wata kofa banda ta Ali (a.s), Magazili ya ambace shi a manakib dinsa, a babin manakibu Ali (a.s).

Na biyar: A al’amarin â€کyar Hamza bn Abdulmudallib.

Na shida: A almarin kwana a cikin masallaci da ya hana kowa kwana a ciki sai shi.

Na bakwai a hadisin Ummu Salama da ya gaya mata game da Ali, Kamar yadda ya zo a littafin tarihi damishk.



back 1 2 3 4 5 6 next