Tattaunawa Ta BiyarIdan ka kasance kamarsa to ina ganin babu amfani ka ci gaba da muhawara, domin yana cewa ne: Rawafidhawa (yana nufin Shi'a) sun kasa tabbatar da imanin Ali (a.s) da adalcinsa. Ya ci gaba da cewa: idan sun kafa mana hujja da cewa akwai tawaturin zance kan musuluncinsa da hijirarsa da jihadinsa, to ai mu ma muna da tawaturin musuluncin Mu'awiya da Yazid da halifofin Banu Umayya da Banu Abbas da sallarsu da azuminsu da jihadinsu kan kafirai… duba: min hajussunna 2: 62. A wani waje yana cewa: Sam babu tabbacin kafirai ko munafukai suna kin Ali (a.s) minhajussunna 7: 461. Ya ce: Ali bai muzanta wa wani ba daga cikinsu (kafirai ko munafukai) a jahiliyya ko a musulunci, domin wadanda ya kashe a yaki duka kanana ne ba manyan kafirai ba ne. ya ce: Umar ma ya fi shi gaba da su. Amma da ya ga dai wanda yake kushewa ya kashe da yawa koda kuwa ya kira su kanana ne, kuma wanda ya yaba bai taba kashe koda daya ba, sai ya ce: Ali an ji ya kashe kafirai da takobinsa amma ba duka ya kashe ba, ya kashe wasu ne daga cikinsu, kuma sahabbai ma kamar Umar da Zubair da Hamza da Mikdad, da Abu Dalha, da Barra, kowa ya kashe kafirai. Da ya ga babu wani tarihin da ya yi daidai da maganarsa sai ya ce: Umar ya kashe kafirai mana domin shi ma ya yi addu’a Allah ya kashe su, kuma yaki ba sai da takobi ba domin yaki da addu’a kamar yaki da takubi ne! Minhajussuna: 4: 480. Ka duba ka ga yadda ake mummunan tawili ta krfin tsiya sai an nuna Imam Ali (a.s) bai yi wa musulunci wani abin kirki da ya cancanci yabo ba. Idan kai ma kamar haka kake, to sai in hutar da alkalamina, idan ka gaya mini matsayinka sai in san da wa nake magana kan Ahlul Bait (a.s) shin da mai gaba da gidan ne, ko kuma mai neman sanin gidan mai neman gaskiya. Ka ga ke nan babu amfani ga wanda ya shata layi, yana ganin mabiyan Ali (a.s) ba zasu iya kawo hujja kwakkwara a kan ma musuluncinsa ba tukun balle a zo maganar jagora ne daga Allah (S.W.T) bayan Annabi (s.a.w)!. Amma game da cewa; Imam Ali da 'ya'yansa (a.s) ba su nuna wa mutane kabarin Sayyida Fadima ba (a.s) da nuna cin mutunci ne hakan kansu, da nuna cewa; zagi ne garesu hakan da kuma ga Annabi (s.a.w), kai da mayar da magana kan bautar kabari: Ban sani ba shin za a yi wa maganar nan taka dariyar ne ko kuma kuka, Ina ganin idan ka kasa sai ka nemi taimakon malamanka, mene ne ya same ka haka kake cakuda maganganu iri-iri waje daya. Na daya: Ka jahilci cewa mutum yana iya wasiyya yadda ya so idan zai mutu matukar ba ta saba wa addinin ba. Kuma Fadima dai â€کyar Manzo (s.a.w) da ita da mijinta da â€کya’yanta, ba ka isa ka nuna masu yadda zasu yi addinin ba, kuma ita ta yi musu wasiyya da boye kabarinta, ko kai ma kana bakin cikin matakin da ta dauka ne! Na biyu: Me ya kawo bautar kabari, wane musulmi ne ka gani ya riki kabari Ubangijinsa abin bauta?! Na uku: Ban taba sanin ka yi nesa da sanin tarihin addini ba sosai sai da na ga wannan magana taka, ka sani kabarin Ibrahim (a.s) ba boye yake ba, kuma an je janazarsa kuma an yi masa salla, sannan kabarin yana nan Bakiyya kuma yanzu haka ina da taswirar duk inda kaburburan nan suke a Bakiyya duk da wahabiyawa sun rusa duka kaburburan bayin Allah da yake wajen karni guda da rabi da ya wuce. Haka ma kabarin Sayyida khadija (a.s) ba wanda ya boye shi, domin babu wata hikimar yin hakan sabanin kabarin Sayyida Zahara (a.s). Wannan kage ne ka yi wa Annabi (s.a.w) na cewa ya boye su, kuma wannan kagen idan daga gareka yake to ka yi hattara ka nemi gafara a kai, idan kuwa wani ya gaya maka ka ce da shi ya nuna maka inda ya samu wannan, idan bai yi ba ka sani shi mai karya ne ga fiyayyen halitta!.
|