Hada Salloli Biyu



Nawawi ya ce: Daga ciki akwai wanda ya yi tawili a kan cewa saboda uzuri ne na rashin lafiya da makamantansu, kamar Ahmad dan Hanbal da Alkali Husain da Khidaibi da Mutawwali da Ruyani[28].

Wasu malamai sun yi raddin wannan tawili, yayin da suke cewa: Idan da ya zama saboda rashin lafiya da ba wanda zai yi salla tare da Manzo sai maras lafiya, wanda kuma a zahiri ya yi jam’i da sahabbansa, kuma wannan shi ne abin da Ibn Abbas ya fada a sarari[29].

Al’amari Na Biyar: Abubuwan Da Suke Karfafar Hadawa

Akwai dalilai da dama da suke karfafa ra’ayin da yake halatta hada sallolin a zaman gida, daga cikinsu a kwai:

1- Ma’abota sahihan littattafan ban da buhari sun ware wani babi a littattafansu da sunan “Hada salloli biyu” sun kuma kawo ruwayoyi da suke nuna halarci da rangwamen haka, sai wannan ya zama dalili a kan hadawa a zaman gida da tafiya da uzuri ko ba uzuri[30]. Da ba haka ba ne da sun ware babi na musamman game da hada salloli a zaman gida da kuma babi na musamman game da hada salloli a lokacin tafiya, sai ya zama sun kawo ruwayoyi ne kai tsaye ba kebancewa. Kuma idan Buhari bai yi haka ba, abin da sauran suka yi ya wadatar kamar Muslim da Tirmizi da Nisa’i da Ahmad dan Hanbal da Masu sharhin Muslim da buhari, kuma buhari ya kawo wasu hadisai sai dai karkashin wasu maudu’ai daban.

2- Fatawar malamai da rashin halarcin hadawa ba tare da wani kebewa ba, ta ginu ne a kan wasu tawiloli da ba su da wani asasi daga wadannan ruwayoyi. (Sai don tawaili na kashin kansu domin ya yi daidai da mazhabobinsu).

3- Shelantawa a fili da ma’abota sihah suka yi cewa Manzo ya yi haka ne domin kada wani daga al’ummarsa ya wahala, wannan yana nufin an shar’anta hadawa domin saukaka mata da rangwantawa babu wani kebancewa, da kuma rashin wahalar da kai saboda rarrabawa, sannan hadisan da suka yi magana game da hadawa alokacin safara ba sa takaita da lokacin safara domin su hadisai sakakku ne ba su da kebewa, kuma ba ma’ana batun tafiya ya shigo cikinsu ko rashin lafiya ko ruwan sama ko tabo ko tsoro, su wadannan ruwayoyi sun shafi kowane yanayi kuma suna aiwatuwa a kowane yanayi kuma a kowane lokaci[31] kamar yadda Karin bayani zai zo a bahasin al’amari na shida.

4- Malamai sun halatta hadawa a zaman gida.

Nawawi yana cewa: Wasu jama’a daga malamai sun halatta jam’i a zaman gida ga mai bukatar hakan idan bai dauke shi al’ada ba, wannan kuma shi ne maganar Ibn Sirin da Ash’habu daga sahabban Maliku, da kuma Hidabi daga Kifal da sahabban Shafi’i da kuma Abu Ishak Maruzi da kuma wasu malamai daga malaman hadisai kuma shi ne maganar Ibn Munzir.

Ya ce: Wannan kuma maganar Ibn Abbas: “Yana son kada al’ummarsa ta wahala” yana karfafarsa, domin bai sanya dalilinsa rashin lafiya ba ko wani abu da su masu tawili suke kawowa.

Wannan magana da yawa daga malamai sun ambace ta kamar Zurkani a sharhin Muwadda da Askalani da Kisdi da wasunsu na daga mutanen da suka yi taliki a kan hadisin Ibn Abbas game da hada salloli biyu[32].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next