Hada Salloli Biyu



A babin sallar issha yana cewa: Daga Ibn Umar da Abu Ayyuba da Dan Abbas: “Annabi (S.A.W) ya yi sallar magariba da issha a hade a lokacin dayarsu”[23].

Abin da dan mas’ud ya karbo yana karfafar wannan yayin da yake cewa; “Annabi ya hada sallar (a Madina) azahar da la’asar, da kuma magariba da issha, sai aka tambayi Manzo (S.A.W) me ya sa hakan, sai ya ce: Na yi ne domin kada al’ummata ta wahala”[24].

Al’amari Na Hudu: Masu Sharhin Muslim Da Buhari

[Suna Kawo Dalilin Halarcin Hada Salla A Zaman Gida Daga Wannan Ruwayoyi Da Cewa Domin Kada Al’umma Ta Wahala Ne]

Nawawi ya tattauna a sharhin Muslim game da tawilin wannan ruwayoyi da suka gabata bisa fassarar asasin mazhabobi, ga abin da yake cewa:

Malamai suna da tawili ga wannan hadisai bisa mazhabobinsu, daga cikinsu akwai wanda ya yi tawili bisa cewa an hada salla ne saboda ruwan sama, ya ce wannan ya shahara gun wasu jama’a daga magabata[25].

Ya ce wannan mai rauni ne kwarai da ruwayar Dan Abbas da take cewa: “Babu wani tsoro ko ruwan sama”. Daga cikinsu akwai wanda ya yi tawili a kan cewa saboda ruwa ne sai ya yi sallar azahar, sannan sai hadari ya tafi sai ta bayyana lokacin la’asar ya yi sai ya yi ta. Wannan kuma batacce ne domin idan sun yi wannan tawili ga azahar da la’asar to me zasu ce game da magariba da issha.

Ya ce: Daga cikinsu akwai wanda ya ce ya jinkirta ta farko ne zuwa karshen lokacinta sai ya yi ta, yayin da ya gama sai ya zama lokacin la’asar ya shiga sai ya yi ta sai ya zama ya yi wani hadi tsakaninsu hadi suri. Ya ce: Wannan ma mai rauni ne kwarai, domin ya saba wa zahirin hadisi sabawa mai tsanani.

Ya ce: Aikin Dan Abbas yayin huduba, sai mutane suka rika cewa salla-salla, da kuma rashin kulawa da su da dalilin da ya kafa da wannan hadisi domin nuna aikinsa daidai ne da jinkirtawar sallarsa zuwa lokacin issha, da kuma hadawa gaba daya a lokacin ta biyu, da kuma gasgatawar da Abu huraira ya yi masa da rashin musawarsa, bayani ne a fili da yake nuna raunin wadannan tawilolin[26].

Akwai raddin wannan tawiloli da Bn Abdulbar ya yi da kuma khadabi da wasunsu da cewa: Hadawa din rangwame ne ga al’umma, da ya kasance jam’i ne suri, da ya fi wahala da ka zo da ita a lokacinta {domin jam’in suri ya fi ma rarrabawar wahala}, domin kula da zuwan karshen lokacin (ta farko) da kula da farkon lokacin (ta gabanta) wani abu ne wanda masana da malamai ba zasu iya gane shi ba ballantana sauran mutane.

Suka ce: Hadawa ba komai take nuna wa ba sai rangwame, fadin Dan Abbas: Yana son kada ya wahalar da al’ummarsa, suka ce hadisan sun nuna gabatar da hadawar tare a lokaci guda ko a lokacin ta farko ko kuma a lokacin ta karshe, wannan kuma shi ne abin da ake fahimta daga ma’anar hadawa, wannan kuma shi ne mahallin da ake jayayya akai[27].



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 next