Marhalar karshen zamani da cin nasarar gaskiyaMas’alar Mahadi (A.S) abu ne wanda masanan Ahlussunna kamar Ibn Abil Hadid[11], da Ibn Khaldon, da Ibnl Arabi suka yarda da shi kamar yadda masu ruwayar hadisai suka yarda da ita, Ibn Khaldon duk da ya raunata hadisai kusan 25 daga cikin hadisan da suka zo game da imam Mahadi (A.S), amma ya yarda da batun zuwan imam Mahadi (A.S) kamar yadda yake fada: Mu sani cewa shi al’amari ne da ya shahara tsakanin dukkan musulmi a tsawon tarihi, kuma akwai imani da cewa lallai a karshen zamani wani mutum daga Ahlul Bait (A.S) zai bayyana…[12] Haka nan Ibnl Arabi ya kawo bayani game da bayyanar imam Mahadi (A.S) wanda yake daga zuriyar imam Ali da fadima (A.S) a karshen duniya da zai cika ta da adalci bayan an cika ta da zalunci[13]. A takaice dai muna cewa: Al’amrin imam Mahadi (A.S) al’amari ne da dukkan musulmi suka yi imani da shi[14], sai dai bambanci shi ne; Ahlussunna suna ganin har yanzu ba a haife shi ba[15], amma Shi'a suna ganin an haife shi, kuma shi ne imami na goma sha biyu, yana rayayye a cikin mutane kamar Hidr (A.S), kodayake a cikin Ahlussunna akwai masu imani da samuwarsa a raye kamar yadda Shi'a suka yi imani da shi. Duk da isgili da ake samu game da wannan mahanga ta Shi'a daga bangaren mulhidai masu musun Allah, amma a nan gaba a karshen duniya wannan mahanga zata tabbata. Idan muka duba ruwayoyin da suka zo game da imam Mahadi (A.S) zamu samu mamaki maras misali na karama da daraja na Manzo (S.A.W) da imamai na cewar yaya suka iya yin bayanin duniya a karshen zamani duk da kuwa samun tsawon lokaci tsakaninsu da wannan zamanin. Suna bayanin karshen duniya kamar suna nan tare abin yake faruwa. A hadisan Shi'a wadanda suke daga duniyar gaibi da wahayi an yi bayanin yanayin tattalin arziki, da siyasa, da zamantakewa, da tafiyar da ikon shugabanci a karshen zamani dalla-dalla. Game da mai tseratar da duniya a karshen zamani mahangar Shi'a ba kamar sauran mahangai ba ce, Shi'a sun yi bayanin game da shi dalla-dalla ne da zurfinsa, da tantancewarsa tun daga nasabarsa da rayuwarsa, da yadda aka haife shi da buyansa har zuwa bayyanarsa, da nau’in hukumarsa da sharuddanta, da waziransa da masu taimaka masa, da dukkan abin da zai faru kafin bayyanarsa da bayanta. Don haka mahangar Shi'a game da imam Mahadi (A.S) tana da kebantattun siffofi na musamman da wata mahanga ba ta da su. Za a kafa daula madaukakiya a karshen duniya da ta saba da mahangar mulhidai da ‘yan jari-hujja. A wannan bangaren zamu yi kokarin bayanin kebantattun al’amuran mahangar Shi'a da bambancinta da sauran mahangai, sannan sai bayanin mahangar Shi'a game da karshen zamani a dunkule ta biyo baya, sannan daga karshe sai bayanin daular karshen zamani.
[1] - Goftumane Mahdawiyyat, Shafi: 136 – 137.
|