Marhalar karshen zamani da cin nasarar gaskiyaMahangarShi'anciGame Imam Mahadi (A.S)
Acikin masu bayanin karshen zamani, musulunci ne kawai shi ma a mazhabar Shi'anci ya yi bayanin dalla-dallan wannan al’amari da zurfi. Ta yiwu wasu su yi tsammanin cewa imamanci shi ne asalin abin da ya zo da batun imam Mahadi (A.S), amma wannan ra’ayi ba daidai ba ne, domin sakon Manzo (S.A.W) shi ne ya fara zuwa da batun imam Mahadi (A.S) kamar yadda muka kawo ayoyi masu yawa daga kur’ani game da al’amarin, haka nan daruruwan ruwayoyi sun shaida da akidar zuwan imam Mahadi (A.S), shi ya sa ma musulmi suka yi imani da zuwan Mahadi (A.S) daga ‘ya’yan Ali (A.S) da Fadima (A.S), kuma sunansa da kinayarsa irin na Manzo (S.A.W) ne[1]. Asalin imani da zuwa imam Mahadi (A.S) ya faro ne daga ruwayoyi tun zamanin Manzo (S.A.W) wanda ya zo da bayani a fili yankakke daga annabi (S.A.W) game da Mahadi mai zuwa karshen zamani, wannan kuwa yana nuda dalilin ingancin mahangar Shi'a[2]. Tawaturyana daga cikin abin da yake nuna ingancin magana ta yadda tsammanin karyar magana zai koru, idan mun duba zamu ga hadisan da suka yi bayni game da zuwan Mahadi (A.S) suna da tawaturta ta yadda hankli ba ya wani kokwanto wajan karbarsu. AllamaDiba’diba’i yana cewa: Idan aka bi kididdiga za a samu sama da ruwayoyi 3000 da suka zo daga annabi da imamai (A.S) game da zuwan imam Mahadi (A.S)[3]. Malaman Shi'a gaba dayansu sun tafi a kan tawaturancin ruwayoyin da suka zo game da imam Mahadi (A.S), haka nan shafi’i ya tafi a kan hakan. Kuma an rawaito hadisai masu yawa game da imam Mahadi (A.S) daga malamai masu yawa na Ahlussunna kamar; Ahmad, Ibn Dawud, Ibn Majah, Tirmizi, Bukhari, Muslim, Nisa’i, Baihaki, Mawardi, Dabrani, Sam’ani, Ibn Sari, Ibn Asakir, Kisa’i, Ibn Asir, Hakim, Ibn Jauzi, Ibn Abil Hadid Mu’utazili, Ibn Sabbag Maliki, Ibn Magazili Shafi’i, Muhibbuddin Dabari, Shabalanji da …, a takaice bayyanar imam Mahadi wani abu ne da aka yi ittifaki a kansa[4]. A wasu ruwayoyin ma an ambaci sunansa da sunan babansa a matsayin cewa shi dan imam Hasan Askari (A.S) ne[5]. Daga cikin manyan littattafai akwai littafin “masnad Ahmad bn Hambal†wanda ya mutu a shekarar 241H, a kwai hadisai game da imam Mahadi da ana iya samun su a jildi (mujalladi) na daya da na biyu, da na uku, da na biyar[6]. Ma’abota littattafai shida na sihahussitta da Ahmad dan Hambal sun rawaito hadisai daga Umar dan Haddabi, da Abdullahi dan Mas’ud, da Abdullahi dan Umar, da Abdullahi dan Abbas, da Sauban, da Jabir dan Abdullahi Al’ansari, da Jabir dan Samura, da Abdullahi dan Amru, da Anas dan Malik, da Abu Sa’idul Khuduri, da Ummul muminin Ummu salama (R.A) da wasunsu[7]. Mas’alar karshen zamani tana daga cikin mas’alolin farko na asasi a musulunci bayan tauhidi, da annabta, da ranar kiyama, kuma babu wani bahasi da aka yi da ya kai na wadannan hadisai[8]. Hatta da malamai a hijaz mas’alar bayyanar imam Mahadi suna ganinta a matsayin mas’ala ta asasin addini ba rassansa ba[9]. Don haka mahadiyyanci idan mun yi la’akari da karshen zamani yana matsayin daya daga laruran addini mai tsarki na musulunci ne, ta yadda wadanda suka yi musun sa suna iya fita daga addinin musulunci: “Wanda ya karyata da Mahadi (A.S) hakika ya kafirtaâ€[10].
|