Ziyartar Kaburbura"Ya Allah ka sanya man haske da tsarki tare, da kuma tsari wadatacce daga dukkan cuta da ciwo da kuma duka bala'i da musiba kuma ka tsarkake zuciyata da gabobina da kashina da namana da jinina, da gashina da fatata, da bargona da kashina da kuma abinda kasa ta rage shi daga gare ni, kuma ka sanya mai shaida gare ni ranar bukatata da fakircina da talaucina." 2- Ya sanya mafi kyawun da mafi tsaftar tufafin da yake da su, domin sanya kyawawa da tsaftatattun tufafi abu ne da mutane ke so wa junansu lokacin bukukuwa, kuma hakan na kusantar da su ga junansu tare da sanya soyayya a tsakaninsu Yana kara sa musu daukaka da jin daukaka a zuciyarsu da jin muhimmancin bukin da suke halarta. Abu da ya kamata mujawo hankali gare Shi a wannan koyarwa Shi ne ba a wajabta cewa dole ne mutum mai ziyara ya sanya mafi kyawun tufafi baki daya ba dungum, a'a sai dai ya sanya mafi kyawun abinda yake da iko kai domin ba kowa ba ne zai iya yin haka, kuma akwai kuntatawa ga raunana wadda tausayawa ba ta bukatar a yi haka, wannan ladabin dai hakika ya gwama tsakanin abinda ya kamata na ado da kuma mafi kyawun tufafin, da kuma kiyaye yanayin fakiri da kuma mai rauni. 3- Ya sanya abinda ya saukaka gare shi na turare, kama fa'idarsa tamkar ta sanya sabin kayace. 4- Ya yi sadaka da abinda ya saukaka gare Shi, kuma fa'idar sadaka a irin wannan al'amari sananniya ce, domin a cikin hakan akwai taimakawa ga gajiyayyu da kuma sanya ruhin tausasawa gare su. 5- Ya tafi Yana cikin natsuwa da kwanciyar hankali Yana mai takaita ganin idonsa. Abinda ke cikin wannan irin natsuwar da girmama alfarmar wannan gurin da kuma wanda ake ziyarta din da kuma mai da hankali ga Allah Ta'ala da yankewa zuwa gare shi, da kuma abinda ke tare da haka din na nesantar damun mutane da matsa musu a yayin wucewa, da kuma rashin munanawa shashensu daga sa she a bayyane yake a sarayi. 6- Ya yi kabbara Yana cewa "Allahu Akbar" ya yi ta maimaitawa yadda ya so, kuma mai yiwuwa ne a wasa ziya rorin a kayyade kabbarar zuwa dari. Akwai fa'ida a cikin yin haka wadda ke sanya wa ruhi jin girman Allah Ta'ala, da kuma cewa babu wani abu da ya fi shi girma, da kuma cewa ziyara ba wata aba ba ce illa ibadar Allah da girmama shi da daukaka shi ta hanyar raya alamun Allah da karfafa addinin shi. 7- Bayan kammala ziyarar kuma ga Annabi ko kuma ga Imami to sai ya yi salla akalla raka'a biyu nafila kuma domin ibada ga Allah kawai, saboda ya yi godiya a kan muwafakar da ya yi masa ya kuma bayar da ladanta ga wanda ya kai wa ziyarar. A cikin addu'ar da aka ruwaito wadda mai ziyarar zai karanta bayan wannan salla akwai abinda zai fahintar wa mai ziyarar cewa wannan salla dai da duk abinda da ya aikata na Allah ne shi kadai da kuma cewa Shi ba ya bauta wa wani baicin Shi kuma ziyarar ba wata abu ba ce face wani nau'in neman kusanci gare Shi Ta'ala. "Ya Allah gare ka na yi Salla, gare ka na yi ruku'u, gare ka na yi sujada, kai kadai ba ka da abokin tarayya, domin babu Salla da ruku'u da sujada sai dai gare ka, domin kai hakika ne Allah babu abin bautawa sai kai. Ya Allah ka yi dadin tsira ga Muhammaddu da zuriyar Muhammadu, kuma ka karba mini ziyarata, kuma ka ba ni abinda na roka, domin Muhammadu da zuriyarsa masu tsarki." A cikin irin wannan addu'ar akwai wani nau'in ladabi da ke bayyana manufofin Imamai da mabiyansu masu koyi da su a ziyartar kabari ga duk wanda ke son ya san hakika, da kuma irin abinda masu jahilta ke kagawa yayin da suke raya cewa wai ziyartarka burbura ibada ce gare su da neman kusanci gare su da kuma cewa shirka ce da Allah a ibada. 8- Daga ladubban ziyara akwai cewa: Mai ziyarar ya Lizimci kyautata abota da duk wanda ya zama tare da shi, da kuma karanta magana, sai dai abinda yake alheri, da yawaita zikirin. Allah, da kankan da kai, da yawaita salla, da salati ga Annabi Muahmmadu da Zuriyarsa kuma ya runtse idandunansa, kuma Ya gaggauta zuwa gurin mabukata daga cikin yan'uwansa idan ya ga abubuwa gare su sun yanke, kuma Ya taimaka musu, ya kuma nesanci abinda aka hana, da kuma husuma, da yawaita rantsuwa da jayayyar da ta hada da rantse-rantse. Sa'an nan kuma alal hakika ziyara ba wata aba ba ce face salati ga Annabi ko Imamai Iyalan Manzon Allah".) Hafizu Muhammad Sa’id Kano Nigeria.
|