Ziyartar KaburburaZiyartar Kaburbura
Ziyartar kaburburan Annabi da na Imamai (AS) da katange su da kuma yin gine-gine a kansu na daga cikin manyan al'amura da mazhabar Shi'a Imamiyya (Masu bin Imamai 12) ta kebantu da su kuma suna bayar da dukan abu mai tsada da mai sauki cikin imani da dadin zuciya. Asalin duk wannan kuma shi ne wasiyyar Imamai da kuma zaburar da mabiyansu da kuma kwadaitar da su a kan irin ladan da take da shi mai yawa a gurin Allah Ta'ala, saboda kasancewarta mafificiyar ayyukan biyayya da ibadu bayan ayyukan ibadu wajibai da kuma cewa adan na kaburburan na daga cikin mafifitan guraren amsa addu'a da ,juyawa ga Allah Ta'ala. Kuma suka sanya ta daga cikin ainihin cika alkawura ga Imamai, domin, "ga kowane imami akwai alkawarinsa a kan majibintansa da mabiyansa, da kuwa cewa daga mafificin cika alkawari, ziyartar kaburburansu na daga mai kyawun cikawa, duk wanda ya ziyarce su yana mai kwadayin haka da kuma gaskata abinda suka kwadaitar a kai, to su Imaman nasu za su kasance masu ceto gare su ranar 'alkiyama."A cikin ziyartar kaburbura akwai fa'idoji na addini da zamantakewa da suka sa Imamanmu himmantuwa da ita, domin a halin cewa a Iokacin da take kara kulla walaya da soyayya tsakanin Imaman da mabiyansu tana kuma sabunta tuna hadisansu da dabi'unsu da jihadinsu saboda gaskiya kuma tana hado kan musulmi wadanda suke warwatse ta tara su guri guda, domin su san juna kana kuma ta dasa ruhin jawuwa zuwa ga Allah a cikin zukatansu da yankewa zuwa gare shi, da bin umarce-umarcensa tana kuma cusa musu hakikanin tauhidi a cikin ma'anonin addu'o'in ziyarorin da ke cike da fasaha wadda aka samo daga Ahlul Bait (A.S.) tare da koya musu tsarkin musulunci da sakon Muhammadu (SAW) da abinda ya wajaba a kan musulmi na daga matabbatan halayen kwarai, da kan kan da kai ga mai tafi da halittu, da gode wa ni'imominsa, don haka ta wannan bangaren tana amfani ne irin na addu'o'in da aka ruwaito wadanda bayaninsu ya riga ya gabata. Kamar yadda wadannan ziyarorin da aka ruwaito suke fahintar da matsayin imamai (A.S.) da irin sadaukarwarsu a tafarkin taimakon gaskiya da daukaka kalmar addini da dagewarsu a ibadar Allah Ta'ala, ga shi kuma sun zo da salon larabci zalla, da fasaha madaukakiya, da ma'anoni masu sauki wadanda kowa da kowa yake fahinta, kuma suna kunshe da mafifitan ma'anonin tauhidi kuma mafi zurfi tare kuma da addu'a da yankewa zuwa gare shi Ta'ala. Alal hakika ita tana daga cikin mafi ingancin laduban addini bayan Alkur'ani mai girma da Nahjul Balagha da kuma addu'o'in da aka ruwaito daga garesu (A.S.) domin a cikinta an kunsa dukan sanin Imamai (A.S.) a takaice dangane da abinda ya shafi wannan sha'ani na addini da gyaran zuciya. Sa'an nan kuma a cikin ladubban ziyarar akwai koyarwa da shiryarwar da ke karfafa tabbatar da wadannan ma'anonin addini madaukaka wato irinsu daukaka tsarkin ruhin musulmi, da koya wa ruhinsa tausasawa ga fakiri, da sanya shi tausasawa ga fakiri, da iya zama da jama'a da kyawun hali, da son cudanya da jama'a, domin daga ladubanta akwai abinda ya kamata a aikata kafin a fara shiga cikin ginin makabartar domin ziyartarsa. Daga nankuma akwai abinda ya kamata a yi a tsakiyar ziyarar da kuma bayan ziyarar. A nan za mu kawo wasu daga cikin wadannan laduban domin fadakarwa a kan abubuwan da take nufi kamar yadda muka fada: Daga Ladubbanta: 1- Mai ziyarar ya yi wanka yayin fara ziyararsa ya tsarkaka, fa'idar wannan kuwa kamar yadda muke fahinta a sarari yake, ita ce mutum ya tsarkake jikinsa daga kazanta domin ya kubutar da shi daga cututtuka da kuma domin kada mutane su gundara da warinsa kazalika kuma ya tsarkake kansa daga kazanta. Ya zo a hadisai cewa mai ziyara ya karanta wannan addu'a idan ya gama wanka domin ya fadakar da shi a kan wadannan manufofi madaukaka ya ce:
|