Musulunci



Kazalika ma sauran hukunce-hukuncen, wannan kuwa yana daga adalcinsa da kuma tausasawarsa ga bayinsa kuma lalle babu makawa Ya zamanto yana da hukunci a kan kowane al'amari,babu wani abu daga cikin abubuwa da zai zamanto ba shi da hakikanin hukuncin Allah a kansa koda kuwa tafarkin saninsa a toshe yake gare mu kuma har ila yau muna cewa lalle yana daga mummunan abu Ya zamanto Ya yi umarni da aikata abinda yake akwai cutarwa a cikinsa, ko kuma Ya hana abinda akwai maslaha a cikinsa.

Sai dai kuma wasu daga cikin bangarorin musulmi suna cewa: Mummunan abu shi ne kawai abinda Allah Ta'ala Ya hana: kyakkyawa kuwa shi ne abinda Ya kyautata kuma Ya yi umarnin aikatawa, ba wai ainihin maslaha da cutarwar a ayyukan suke ba, kuma babu kyawu ko rashin kyawu a ainihin zatin Wannan batu kuwa ya saba wa abinda hankali Ya wajabta.

Kazalizaka sun halatta cewa Allah na iya aikata mummuna Ya yi umarni da bu wanda akwai cutarwa a cikinsa kuma ya hana abinda yake akwai maslaha a cikinsa, Ya riga Ya gabata cewa wannan irin magana akwai rashin girmamawa a cikinta kwarai. Saboda wannan magana na hukunta danganta jahilci da gazawa ga Allah, (Allah ta’ala Ya daukaka, daukaka mai girma ga barin irin wadannan al’amura).

A takaice dai: Abinda yake sahihi a akida shi ne, mu ce shi Allah T'a'ala ba Shi da wata maslaha ko fa'ida a kallafa wajibai da kuma haramta haramtattu sai maslahar da fa'idojin duka suna komawa ne gare mu a dukan ayyuka, Kuma babu wata ma'ana wajen a kore maslaha ko barna game da ayyukan da aka yi umarni ko aka hana aikatawa. Allah ba Ya umarni don wasa ba Ya hani haka banza shi kuma mawadaci ne ga barin bukatar bayinsa.

Wajabta Aiki

Mun yi imani cewa Allah Ta'ala ba Ya kallafa wa bayinsa aiki sai bayan Ya tabbatar musu hujja a kansu kuma ba Ya kallafa musu sai abinda za su iya aikata shi kuma suke da ikon aikata shi kuma suka san shi domin yana daga zalunci kallafa aiki ga ajizi, wanda ba zai iya ba, da kuma Jahilin wanda ilimi bai isa zuwa gare shi ba, ba wai Ya ki neman ilimin da ganganci ba.

Amma shi kuwa Jahili wanda Ya ki neman sani da gangan alhali yana da damar samun ilimin hukunce-hukunce da ayyukan ibada to shi ne mai amsa tambaya a gurin Allah Ta'ala, kuma shi za a yiwa ukuba a kan sakacinsa domin wajibi ne a kan kowane mutum Ya koyi abinda yake bukata    na daga hukunce-hukuncen shari'a.Kuma mun yi imani cewa: shi Allah Ta'ala babu makawa Ya kallafa wa bayinsa ayyuka Ya kuma sanya musu shari'o'i abinda na amfani da kuma alheri gare su a cikinta domin Ya sanya su a kan hanyoyin alheri da rabauta dindindin, sa'an nan kuma Ya shirye su zuwa ga abinda Yake shi ne maslaha kuma Ya gargade su game da abinda yake akwai fasadi da barna a cikinsa da kuma cutarwa gare su

da kuma mummunan karshe gare su. Koda kuwa Ya san cewa su ba za su bi Shi ba, domin wannan tausasawa ne da kuma rahama ga bayinSa don kasancewarsu sun jahilci mafi yawancin amfanin kansu da hanyoyinsu a nan duniya da kuma lahira. Sun jahilci da yawan abubuwan da za su jawo musu cuta da hasara, Shi kuwa Allah Ta'ala Shi ne Mai Rahama mai Jin kai a ainihin zatinSa, Shi kamala ne tsantsa wanda kuma shi ne ainihin zatinSa kuma  har abada bai rabu daga gare shi.Wannan tausasawa kuwa ba za ta gushe ba, don bayinsa sun kasance sun bijire sun ki bin sa, sun ki kayyaduwa da umarce­umarcensa kuma sun ki hanuwa da hane-hanenSa.

Hafizu Muhammad Sa’id Kano Nigeria.

 



back 1 2 3