MusulunciA yau da kuma gobe musulmi ba su da wata mafita illa su koma ga kawukansu su yi wa kansu hukunci a kan sakacin da suka yi Su yi yunkurin gyara kansu da zuriyoyi masu zuwa ta hanyar ba su koyarwar addininsu mai inganci domin su gusar da zalunci da ja'irci tsakaninsu. Da haka ne kawai za su tsira daga wannan halaka mai girma kuma babu makawa daga bisani a cika kasa da adalci daidaitawa bayan an cika ta da zalunci da munanawa kamar yadda Allah Ta'ala Ya yi alkawari. "Kuma lalle mun rubuta a littafi bayan ambato cewa kasa bayina salihai ne masu gadon ta, Lalle a cikin wannan akwai isarwa ga mutane masu ibada." Surar Anbiya'i: 105-106. Hadisai kuma sun zo da silsila daban-daban har zuwa kan Manzo (S.A.W.) da kuma Imamai (A.S) cewa Mahadi (A.S) daga 'ya'yan Fatima (A.S) zai bayyana a karshen zamani domin ya cika duniya da daidaitwa da adalci bayan an cika ta da zalunci da rashin daidai. Babu makawa wani Imami ya zo ya kakkabe wa Musulunci abinda aka lillika masa na daga bidi'a da bata kuma ya tserar da bil Adama, Ya kubutar da su daga abinda suka kutsa ciki na daga fasadi gama gari da zalunci mai dorewa, da kiyayya mai ci gaba, da izgili da koyarwar kyawawan dabi'u da ruhin dan Adamtaka. Allah Ta'ala Ya gagagauta bayyanarsa Ya saukake hanyar bayyanarsa. Mai shari’a
Mun yi imani da cewa ma'abucin sakon addinin Musulunci shi ne Annabi Muhammadu dan Abdullahi kuma shi ne cikamakin Annabawa shugaban Manzanni, kuma mafificinsu baki daya, kamar kuma yadda shi ne shugaban Bil Adama baki daya. Babu wani mai falala da ya yi daidai da shi, babu wani da ya yi kusa da shi a karimci babu wani mai hankali da zai yi kusa da shi a hankali babu wani kamar shi kuma a kyawawan dabi'u kuma shi yana kan manyan kyawawan dabi'u, Allah Ta'ala Yana cewa: "Lalle kana kan manyan halayen kwarai masu girma." Surar 11- kalam: 4. Wannan kuwa tun daga farkon tasowarsa ne har zuwa ranar tashin Alkiyama. Amirul muminina Aliyyu Bin Abi Talib (A.S.) ya siffanta shi a daya daga cikin hudubobinsa yana cewa: "Ya zabe shi bishiyar Annabawa da fitila mai haske da kuma mai tsororuwar daukaka da mafi darajar gurare, da fitilun haskaka duffai da kuma mabubbugar hikima." Daga cikin wannan hudubar har ila yau Amirul Muminina(A.S) yana cewa: "Likita mai zazzagawa da maganinsa ya shirya kayan aikinsa yana amfani da su duk lokacin da bukata ta kama wajen warkar da makantattun zukata, da kuraman kunnuwa, da bebayen bakuna, yana bibiyar guraren gafala da maganinsa da kuma guraren rudewa, ba su yi amfani da hasken hikima ba, ba su kunna kyastu makoyar ilimi ba, su sun zamanto kamar dabbobi masu kiwo da duwatsu masu tsauri." (Nahajul Balagha Huduba ta 108). Hukunce-hukuncen addini
Mun yi imani cewa Allah Ta'ala Ya sanya hukunce-hukunce wajibai da haram da sauransu daidai da maslaha da alheri ga bayinSa a cikin ainihin su ayyukan, abinda maslaharsa ta zama babu makawa sai da ita Ya sanya shi wajibi wanda kuma cutarwar da ke tare da shi ta kai matuka to Ya haramta shi wanda kuwa maslaharsa ta zama da kadan ta rinjayi cutarwarsa to Ya sanya mana shi mustahabi.
|