Addu’a Ibada ce



Wannan wani irin cusa wa zuciya jin dadin samun kusanci da Allah (S.W.T) ne, da duba zuwa ga karamcinsa da kudurarsa, don soyayya da bege gare shi, da kuma nuna cewa wannan irin jin dadin ya kamata ne ya kai ga darajar da tasirin barinsa a wajan rai ya fi zafin wuta azaba. Idan muka kaddara cewa mutum na iya jure zafin wuta, to da ba zai iya hakuri a kan waccan rabuwar ba, kamar kuma yadda daga wannan bangaren addu’ar za a fahinci cewa wannan soyayyar da jin dadin na kusanci da abin kauna abin bauta shi ne mafificin mai ceto ga mai zunubi a gurin Allah, yadda zai yafe, kuma ya yi masa rangwame. Mamakin taushin wannan salo na kaskantar da kai ga Mai girma, Mai hakuri, Mai karbar tuba, Mai gafarta zunubai, ba zai buya ba.

 Babu Iaifi mu rufe wannan bayani da kawo takaitacciyar addu’a da ta kunshi kyawawan dabi’u, da kuma abin da ya kamata kowace gaba ta mutum ko kowane mutum ya siffantu da su na daga siffofi kyawawa ababan yabo:

“Ya Allah ka arzuta mu da muwafakar da’a, da nesantar sabo, da gaskiyar niyya, da sanin abubuwa masu alfarma, kuma ka girmama mu da Shiriya da tsayuwa daidai, da daidaita harsunanmu, da daidaito, da hikima, ka cika zukatanmu da ilimi da sani, ka tsarkake cikkunanmu daga haram da shubuha, ka kame hannayenmu daga zalunci da sata, ka runtsar da idanuwanmu daga fajirci da ha’inci, ka toshe kunnuwanmu daga jin maganar banza da giba, kuma ka yi falala ga malamanmu da zuhudu da nasiha, ga masu neman ilimi kuma da kokari da shauki, ga masu sauraro kuma da biyayya da wa’aztuwa, ga marasa lafiyar musulmi kuma da waraka da hutawa, ga matattunsu kuma da rangwame da rahama, ga tsofaffinmu kuma da nutsuwa da kwanciyar hankali, ga matasanmu kuma da komowa da yawan tuba, ga matanmu kuma da jin kunya da kamewa, ga mawadatanmu kuma da kaskan da kai da yalwatawa, ga matalauta kuma da hakuri da wadatar zuci, ga mayaka kuma da cin nasara da galaba, ga ribatattun yaki kuma da kubuta da hutawa, ga shugabanni kuma da adalci da tausayawa, ga al’umma kuma da yin daidai da kyawun hali. Ka sanya albarka ga mahajjata da masu ziyara da guzuri da ciyarwa, kuma ka hukunta abin da ka wajabta musu na daga hajji da umra don falalarka da rahamarka, Ya mafi rahamar masu rahamaâ€‌.

Kuma ni ina mai wasiyya ga â€کyan’uwana masu karatu da cewa, kada damar karanta wannan addu’a ta kubuce musu, tare da sharadin yin tunani a kan ma’anoninta da abubuwan da take nufi, tare da halarto da zuciya da fuskantowa zuwa ga Allah da tsoro da kaskan da kai, da kuma karanta ta tamkar yana magana da kansa ne, tare kuma da bin ladubban da aka ambata daga Ahlul Baiti (A.S), Domin karanta ta ba tare da fuskantar da zuciya ba to maganar baka ce kawai, kuma ba ta kara wa mutum sani, ba ta sama masa kusanci, kuma ba ta yaye masa bakin ciki, kuma ba a amsa masa addu’a da haka. “Hakika Allah mai girma da buwaya ba ya karbar addu’a daga zuciya rafkananniya, don haka idan ka yi addu’a ka fuskanto da zuciyarka, sannan ka ji cewa lalle za a amsaâ€‌[1].

Addu’o’in Sahifatus Sajjadiyya

Bayan aukuwar al’amarin karbala mai ban takaici, da kuma kame ragamar shugabancin al’ummar musulmi da Banu Umayya suka yi, kuma suka dulmuya a cikin danniya, suka yi dumu-dumu da jinin mutane, sannan suka yi watsi da koyarwar Addini, sai Imam Zainul Abidin kuma Sayyiddus Sajidin ya zauna a gidansa yana bakin ciki da jin takaici, yana gida babu wani mai kusantarsa, kuma ba zai iya yada wa mutane abin da ya wajaba a kansu ko ya kamata su sani ba.

 Sai ya tilastu a kan ya dauki salon addu’a wanda muka ambata na cewa, yana daga cikin hanyoyin tsarkake zukata a matsayin hanyar yada koyarwar Alkur’ani da ladubban Musulunci, da kuma sanar da tafarkin Ahlul Baiti (AS), kuma hanyar cusa wa mutane ruhin Addini da zuhudu, da abin da ya wajaba na daga gyaran zukata da kuma kyawawan dabi’u.

Wannan hanya ce da ya fare ta a fakaice don koyar da mutane ba tare da ya jawo hankalin azzaluman Shugabanni da suke matsa masa ba, kuma ba zasu iya kafa masa wata hujja ba, don haka ne ya yawaita yin wadannan addu’o’i masu zurfi, kuma an tattara wadansunsu a littafin Sahifatus Sajjadiyya da ake yi wa lakabi da Zaburar Zuriyar Muhammad (S.A.W). Salonta da manufofinta sun zo da siga da salon Larabci mafi daukaka, kuma mafi daukakar addini, da mafi ingancin asiran tauhidi da Annabci, kuma mafi ingancin hanyar koyar da kyawawan dabi’u ababan yabo, da kuma ladubban Musulunci. Kuma ta kunshi maudu’ai daban daban ne na tarbiyya ta Addini da ta shafi koyarwar Addini, da kyawawan dabi’u, ta hanyar addu’a, ko kuma addu’a ce amma da salon koyar da Addini da kuma kyawawan dabi’u. Ita ce salon bayanin Larabci mafifici, kuma mafi daukakar mashayar manufar sanin Ubangiji da kyawawan dabi’u bayan Alkur’ani da Littafin Nahjul Balagha.

Daga cikinsu akwai wanda yake sanar da kai yadda zaka daukaka Allah kuma ka tsarkake shi, da yabonsa da gode masa da komawa zuwa gareshi. Daga ciki akwai wacce take sanar da kai yadda zaka yi zance da Allah, da kebewa da shi da sirrinka, da yankewa zuwa gareshi, daga cikinta akwai wadanda ke shimfida maka ma’anar Salati ga Annabi (S.A.W) da Manzannin Allah da zababbunSa daga cikin halittunSa, da yadda ake yin sa, daga cikinsu akwai wadanda zasu fahimtar da kai abin da ya dace ka bi iyayenka da shi, da kuma abin da zai yi maka sharhin hakkokin Uba a kan dansa, da na da a kan mahaifinsa, ko kuma hakkokin makwabta, ko na dangi, ko hakkokin musulmi baki daya, ko hakkokin matalauta a kan mawadata da kuma akasin haka. Daga cikin addu’o’in akwai wadanda zai fadakar da kai kan abin da ya wajaba na basussukan mutane akan ka, da kuma abin da ya kamata ka sani na al’amuran tattalin arziki da dukiya, a abin da ya kamata ka yi mu’amala da shi ga abokanka da sauran mutane baki daya, da wadanda kake neman yin mu’mala da su a maslaharka, da kuma abin da zai hada maka dukkan kyawawan dabi’u, kuma ya zama maka tafarki cikakke na ilimin kyawawan dabi’u.

Daga cikinsu akwai wadanda zasu koya maka yadda zaka yi hakuri a kan munanan abubuwan da suke faruwa, da kuma yadda zaka yi yayin da kake rashin lafiya, da kuma yayin da kake lafiya lau. Daga cikinsu akwai wadanda suke yi maka sharhin ayyukan wajibi da suka hau kan sojojin Musulunci da wajiban mutane dangane da su, da dai sauran wadannan da kyawawan dabi’u abin yabo suke farlanta su, duk ta hanyar addu’a.

Abubuwan da suke kunshe cikin addu’ar imam su ne:



back 1 2 3 4 5 6 7 next