Addu’a Ibada ce



Babu shakka cewa misalin irin wannan ikrarin a cikin kadaici ya fi sauki ga mutum a kan ikrari a cikin jama’a, duk da kuwa yana daga cikin mafi tsananin wahalar halaye ga mutum koda kuwa tsakaninsa ne da ransa. Idan da wannan hali zai samu ga mutum, da ya samu sha’ani mai girma na kamala wajan rage takamar kansa mai sharri, da tarbiyyantar da ita akan alheri. Duk wanda yake son tarbiyyar zuciyarsa, to babu makawa ya koyar da ita kadaitaka da `yantaccen tunani domin yi mata hisabi, kuma mafificiyar hanyar wannan kadaitakar ita ce dukufa a kan karanta wadannan addu’o’in da aka samo daga ruwayoyi, wadanda kuma suke ratsa zuciya, kamar karanta addu’ar Abi Hamza Assumali (R.A.)

“Ya Ubangiji ka rufe ni da suturcewarka, ka yafe mini zargina da girman fuskarkaâ€‌. Yi tunani a kan wannan kalma “Ka rufe niâ€‌, a cikinta akwai abin da yake tayar wa zuciya kwadayin suturce abin da ta tattara a kai na mummunan aiki, domin mutum ya fadaka a kan wannan al’amari, ta yanda kuma zai san haka idan ya karanta wannan fakara bayan waccan:

“Idan da yau wani baicin kai ya san da zunubina to da ban aikata ba, kuma da na tsoraci gaggauta ukuba da na nisanci zunubinâ€‌. Wannan irin furuci daga cikin zuciya, da kuma fadaka zuwa ga kwadayin suturce abin da yake da shi na daga munana, yana tayar da kwadayin neman gafara da yafewa daga Allah (S.W.T) don gudun kada ya tozarta shi a gurin mutane, idan da Ubangiji ya so ya yi masa ukuba a nan duniya ko kuma a lahira a kan ayyukansa, sai mutum ya dandani dadin addu’ar sirri, da zance da Allah a asirce, ya yanke ya koma ga Allah, ya yi godiya gare shi da ya yi masa afuwa alhalin yana da kudura amma bai fallasa shi ba yayin da yake cewa:

“Godiya ta tabbata gareka a kan hakurinka bayan saninka, da yafewarka bayan kudurarkaâ€‌. Sannan kuma addu’ar ta sake nuna wa rai tafarkin neman uzuri daga abin da ta yi sakaci dangane da shi saboda wannan afuwa da hakuri daga gare shi (S.W.T), domin kada alakar da take tsakanin bawa da Ubangijinsa ta yanke, kuma domin koya wa bawa cewa sabonsa ba wai don kafirce wa Allah ba ne ko kuma wulakanta umarninsa, yayin da yake cewa:

 Ã¢â‚¬Å“Kuma hakurinka gare ni yana dauka ta yana ja na zuwa ga saba maka, kuma Suturcewarka na kira na zuwa ga karancin jin kunya, kuma sanina game da yalwar rahamarka da girman afuwarka yana gaggautar da ni zuwa ga kifuwa a kan abubuwan da ka haramtaâ€‌.

Wannan shi ne tsarin salon addu’ar a ganawa ta asirce ta tsakake zukata, da saba musu, da da’a, da barin aikata sabo. Wannan littafi ba zai wadatar ba ya kawo irin wadannan misalai fiye da haka alhalin ga su da yawan gaske.

 Salon tattaunawa da Ubangiji domin neman afuwa da gafara yana kayatar da ni, kamar yadda ya zo a Addu’ar Kumail Bn Ziyad:

“Kuma kaicona! Ya shugabana majibincina! Ashe ka sallada wuta a kan fuskokin da suka kifu ga girmanka suna masu sujada, da kuma a kan harsunan da suka yi furuci da gasgatawa, kuma suna yabo da godiyarka, da kuma a kan zukata da suke neman ilimi game da kai har suka zamanto masu tsoro, da kuma gabobi da suka yi kokari zuwa guraren ibadarka suna masu biyayya, suka kuma yi ishara ga afuwarka suna masu mika wuya? Ba haka zato yake game da kai ba, ba kuma mune muka fi sanin falalarka ba.â€‌

Ka maimaita karanta wannan fakara sannan ka yi tunani game da taushin wannan irin kafa hujjar da kololuwar fasaharsa, da azancin bayaninsa, a lokaci guda yana mai sanya wa zuciya furuci da takaitawarta ga ibada, kuma tana cusa mata rashin debe tsammani daga rahamar Allah da baiwarsa, sannan kuma tana yi wa zuciya magana da zance na tausasawa ta wani bangare a boye, domin ya cusa mata sanin manyan wajibanta, domin tana kaddara cewa ita dama ta riga ta ba da wadannan wajibai baki daya, sannan kuma tana koya wa mutum cewa da wadannan ayyukan ne yake cancantar falalar Allah da gafararsa, wannan kuwa wani abu ne da kan zaburar da mutum ya koma ga zuciyarsa don ya aikata abin da ya wajaba a kansa idan har bai aikata shi ba.

Karanta wani salon addu’ar da a ke neman uzuri a cikin ta da cewa: “Ya shugabana majibincina! Ka sani ina iya hakuri a kan azabarka amma ta yaya zan yi hakuri a kan rabuwa da kai! Kuma ko da na iya hakuri a kan zafin wutarka amma yaya zan yi hakuri a kan rashin dubi zuwa ga girmanka!â€‌.



back 1 2 3 4 5 6 7 next