Annabci



[3] - “Manzanni masu bushara kuma masu gargadi domin kada mutane su zama suna da wata hujja a kan Allah bayan Manzanni kuma Allah mabuwayi ne Mai hikima”. Surar Nisa’i: 165.

[4] - “Kuma sai muka yi wahayi ga Musa kan cewa jefa sandarka sai ga shi tana hadiddiye abubuwan da suke kirkira. Kuma gaskiya ta tabbata abin da suke aikatawa kuma ya baci, Sai aka rinjaye su a nan sa’annan suka juya suna kaskantattu, Kuma aka kifar da masu sihirin suna masu sujada”. Surar A’araf; 117-120.

[5] - “Kuma Manzo zuwa ga Bani Isra’ila cewa lalle ni na zo muku da aya daga Ubangijinku ni ina halitta muku daga laka abin da yake kamar surar tsuntsu kuma in hura a cikinsa sai ya zamanto tsuntsu da izinin Allah kuma ina warkar da makaho da mai albaras kuma ina raya matattu da izinin Allah kuma ina ba ku labarin abin da kuke ci da wanda kuke taskacewa a gidajenku lalle a cikin wannan akwai aya gare ku idan kun kasance muminai”. Surar AI- Imran: 49.

[6] - Duba fadin Allah madaukakin sarik:

 â€œKuma idan da mutane da aljannu zasu taru a kan su zo da kwatankwacin wannan Alkur’anin to da ba zasu zo da makamancinsa ba koda kuwa sashensu na taimakon sashe”. Surar Isra’i: 88.

“Ko suna cewa shi ne ya kage shi ne ka ce to ku zo da surori goma makamantansa kagaggu kuma ku kira duk wanda za ku iya wanda ba Allah ba in kun kasance masu gaskiya”. Surar Hud: 13

kalubalantar su kan su kawo sura guda kamarsa:

 â€œKuma idan har kun kasance a cikin kokwanto daga abin da muka saukar to ku zo da sura daya kamarsa kuma ku kira shaidunku da ba Allah ba in kun kasance masu gaskiya”. Surar Bakara: 23

Allah Ta’ala Yana cewa:

 â€œKo suna cewa ya kage shi ne ka ce ku zo da sura guda kamarsa kuma ku kira duk wanda za ku iya koma bayan Allah in kun kasance masu gaskiya”. Surar Yunus: 38.

[7] - Isma shi ne rashin aikata sabo a kowane hali da zamani a rayuwar mai ita, shin a lokacin yarinta ne ko girma ko tsufa, kafin aike da daukar nauyi ko a lakacin hakan.

 



back 1 2 3 4