Annabci



Saboda haka abu ne mawuyaci ga mutum masanin ilimin zamani ya kai kansa ga dukkan tafarkunan alheri da amfani, da kuma sanin dukkan abin da zai amfane shi ko ya cutar da shi a Duniya da Lahira, ballantana kuma jahili. Al’amarin ya kebance shi ne ko kuma ya shafi al’umma da yake zaune a cikinta ne, kuma ba ya iya kai wa ga wannan masaniyar koda kuwa ya hada kai ya yi taimakekeniya da sauran mutane da ke tare da shi, kuma koda kuwa sun hadu sun yi bincike ko sun yi tarurruka da zama daban-daban da kuma shawarwari.

Don haka ne ya zama wajibi Ubangiji ya aiko da Annabawa da Manzanni a cikin mutane domin rahama da tausasawa gare su. “Manzo daga cikinsu yana karanta musu ayoyinSa yana tsarkake su kuma yana koya musu littafi da hikima”. Surar Juma’a: 2. Domin su yi wa mutane gargadi game da abin da yake da cutarwa gare su, da yi musu albishir da abin da yake da alheri, da gyara, da sa’ada, a gare su.

Tausasawar Allah ga bayinSa wajibi ce domin tana daga cikin tsantsar kamalarSa, shi mai tausasawa ne ga bayinSa, mai yawan baiwa, mai karimci, idan kuwa har ya zamanto a wani guri da ya dace akwai bukatar ya kwarara kyautarSa da tausasawa, to babu makawa ya kwararo tausasawarSa domin babu rowa a farfajiyar rahamarSa, babu tawaya a kyautarSa da karimcinSa.

Ma’anar wajibi a nan ba yana nufin cewa wani zai umarce shi da aikata haka ba, sai ya wajabta a kan Allah madaukakin sarki ya bi shi, Allah ya daukaka ga haka daukaka mai girma! Ma’anar wajibci a nan tana daidai da ma’anar fadinka da kake yi cewa shi wajibin samuwa ne wato ba zai taba yiwuwa a kore masa samuwa ko a raba shi da ita ba.

Game Da Mu’ujizar Annabawa

Mun yi imani da cewa yayin da Ubangiji (S.W.T) yake sanya wa bayinsa mai shiryarwa ko manzo, to babu makawa ya sanar da shi gare su ya kuma nuna musu shi a ayyane. Wannan kuwa ya takaita ne a kan sanya musu wani dalili da kuma kafa musu hujja a sakon domin cika tausasawarsa da kuma kammala rahamarsa. Kuma wannan dalilin dole ya kasance ya zo daga mahaliccin halittu mai juya al’amuran samammu[3], wato ya zama abin da ya gagari kudurar dan Adam, sai ya sanya shi a hannun shi Manzon mai shiryarwa domin a san shi da shi, kuma mai shiryarwa zuwa gare shi, wannan dalili shi ake kira mu’ujiza saboda kasancewarsa ya gagari dan Adam ya gudanar da irinsa, ko kuma ya zo da misalinsa.

Kamar yadda babu makawa ga Annabi ya zo da mu’ujiza ya bayyana ta ga mutane domin ya kafa musu hujja, haka nan babu makawa wannan mu’ujizar ya bayyanar da ita ta yadda za ta gagari malamai da kuma kwararrun zamaninsa ballantana sauran mutane, tare kuma da danganta wannan mu’ujizar da da’awar Annabci daga shi mai mu’ujizar saboda ta kasance dalili a kan da’awarsa.

Idan irin wadancan kwararru suka gaza zuwa da irinta sai a sani cewa ta fi karfin ikon dan Adam, kuma ta keta al’ada, daga nan sai a san cewa ma’abocinta yana sama da kudurar dan Adam, kuma yana da alaka da mai juya al’amuran samammu. Idan wannan ya tabbata ga mutum -bayyanar mu’ujiza wadda ta saba wa al’ada- ya kuma yi da’awar Annabci da sako, to sai ya zamanto abin gaskatawar mutane ga kiran da yake yi tare da yin imani da sakon nasa da bin maganarsa da umarninsa, sai wanda zai gaskata shi ya yi imani da manzancinsa da kaskan da kai ga umarninsa, wanda zai yi imani da shi ya yi, wanda kuma zai kafirce masa ya kafirce.

Wannan shi ne abin da ya sa muka ga cewa mu’ujizar kowane Annabi ta dace da abin da ya shahara a zamaninsa na ilimi da fasaha, mu’ujizar Annabi Musa ita ce sanda wanda take hadiye sihiri da abin da suke yin baduhunsa saboda kacancewar sihiri a zamaninsa shi ne fannin fasaha da yake mashahuri, yayin da sandan ya zo sai dukan abin da suke aikatawa ya baci, suka san cewa wannan abu ya fi karfinsu, kuma yana saman fannin fasaharsu, kuma dan Adam ya gajiya ya kawo shi, kuma kwarewa da ilimi sun gajiya a gabansa[4].

Hakanan mu’ujizar Annabi Isa (A.S) ita ce warkar da makafi da masu baras, da raya matattu, saboda shi ya zo ne a lokacin da likitanci ne yake ya yadu a tsakanin mutane, kuma akwai malamai likitoci da suke da kwarewa mai girma, sai iliminsu ya kasa gogayya da abin da Isa (A.S) ya zo da shi[5].

Mu’ujizar Annabinmu madawwamiya ita ce Kur’ani mai girma mai gajiyarwa -ga waninsa na daga fasahohi- da balagarsa da fasaharsa a lokacin da balagar magana ta kasance ita ce fanni sananne, ma’abota ilimin balaga da azancin magana su ne kan gaba a tsakanin mutane da kyawun bayaninsu da daukakar fasaharsu, sai Kur’ani ya zo musu kamar tsawa, ya dimautar da su, ya fahimtar da su cewa su ba zasu iya fito na fito da shi ba. Don haka suka sallama masa rinjayayyu bayan sun gaza gasa da shi, suka ma gaza isa ga kurar da ya tile su da ita ya wuce ya barsu[6].



back 1 2 3 4 next