Aure A Shari'ar Musulunci



"Kuma Matayen da kuka yi Mutu'a dasu, wajibi ne ku basu ladan su (Sadaki)".

Malam Dabariy cikin Tafsirinsa Al-Kabir ya fitar, haka nan Malam Zamakhshari cikin litttafin sa Kashshaf, sannan Malam Raziy a Tafsirin sa, sai Sharhin Muslim na Nawawiy a farkon Babinsa na auren Mutu'a cewar: Ubayyu dan Ka'abu, da Ibn Abbas, da Sa'id dan Jubair, da Ibn Mas'ud da Saddiy suna karanta wannan Aya ne da:

"فَمَا اسْتَمْتَعْتُمْ بِهِ مِنْهُنَّ إِلَى أَجَلٍ مُسَمَّى"

Su suna kara kenan:

"إِلَى أَجَلٍ مُسَمَّى"

Ma'ana:

"Izuwa kayyadajjen lokaci"

Sannan wadannan Malamai dukkanin sun karfafa cewar wannan Ayar ta sauka ne akan Mutu'a: Malam Ahmad bn Hanbali a Musnadin sa, hakanan ma Malam Abubakar Al-Jassas cikin Al-Ahkamul-Kur' an, da Malam Abubakar Al-Baihaki cikin Sunanul-Kubra, da Malam Al-Kadi Al-Baidawiy a Tafsirin sa, da Malam Ibn Kathir a nasa Tafsirin, da Malam Jalaluddin Suyudi a Durrul-Manthur, da Malam Al-Kadi Ashshaukani a Tafsirin sa, da Malam Shihabuddin Alusi a Tafsirinsa, da Sanaduddukan da suke karewa da irin su Ibn Abbas, da Ubayyu dan Ka'abu, da Abdullahi dan Mas'ud, da Imrana dan Hasinu, da Habibu dan Abi Thabit, da Sa'idu dan Jubair, da Kutadatah, da Mujahid.

Bazai iya yiwuwa ace an fassara wannan Aya da cewa tana Magana ne akan auren Da'imi ba, kamar yadda mai Tafsirul-Manar ya karfafa. Dalilin kuwa da yasa hakan bazai yiwu ba shine, zuwan wadannan dalilai:

1-    Abinda ya gabata na daga wani adadin Sahabbai dake karanta wannan Aya da:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next