Aure A Shari'ar Musulunci



A tunanina ni nasan darajar Shehi Wane da iliminsa bazai taba yiwuwa ace ya yarda yana aikata abinda Shari'ar Musulunci bata yarda da shi ba. Don haka ni nake ganin anya kuwa ba suna ninke mutane bai-bai bane, su tsira daga canjin Suna kada a jefesu da wani bangaranci na Addini. Ko kuma Jama'a ta watse ta barsu, dan abin shan miyar da suka saba samu daga Dalibai ko Yara ya sullube musu? Saboda su kansu sun yi tunanin cewar: "KODA YAUSHE DAN ADAM YANA MATUKAR GABA DA ABINDA YA JAHILTA" yasa suce kurum Kwarkwarorine tunda yawancin Al'uma sun tafi akan halascin Kwarkwarori a yanzu. Don haka sai su rika kulla Auren mutu'a dasu, amma a zahiri sai suce Kwarkwarori ne. To abin dai na bukatar dogon Nazari da Tunani. Allah yasa mu dace.

Tunda mun samu cewar ba lallai sai ta hanyar Daurin aure Mace kan halasta ga Namiji har ya Sadu da Ita ba. Akwai wasu hanyoyin daban. To mai zai hana Al'umma ta rika yiwa Mutu'a kallo irin na alakar Kwarkwara? Don haka su ma daina kara kalmar aure din, suce Mutu'a kai tsaye. A matsayin dai itama wata hanya ce da Addinin Musulunci ya halasta ta, Mace da Namiji su gudanar da wata alaka ta Sirri kamar yadda Addini Musulunci

SHIMFIDA

Yana da kyau kafin mu kutsa kai tsaye cikin zurfin ramin bayani kan "Mutu'a", mu dan gangaro da bayani dan kadan akan Shari'a da Hukunci. Dukkanin wata Shari'a ko Hukunci suna farowa ne daga Ubangiji Madaukakin Sarki, daga nan sai Fiyayyen Halittu Annabi Muhammad (Sallallahu alaiHi wa Alihi), amma shima kansa Manzon (Sallallahu alaiHi wa Alihi) sai yayin da akace ne babu wani Hukunci akan abin daga Ubangiji Madaukakin Sarkin, to sannan ne sai ya zartad da nasa Hukuncin akai. Amma yayin da ya zamanto Ubangiji ya yanke nasa Hukuncin akai to bazai yiwu a tashi wannan Hukunci na Allah ba. Haka nan abu ne marar yiwuwa ace Hadisi ya tashi hukuncin Ayar Ubangiji. Domin maganar Manzo in dai har tasa din ce bata sabawa da Maganganun Allah mudlakan.

Sannan kuma bayan Manzo (Sallallahu alaiHi wa Alihi) sai "Fukaha'u" Manyan Malamai wadanda suka kai matsayin "Mujtahidai" , suma sai idan ya kasance babu Hukuncin daga Ubangiji da Manzonsa ne suke da damar shiga cikin Kur'ani da Hadisan Manzo su fitar da Fatawa akan abinda ya taso babu yankakken Hukunci akan sa daga Kur'ani da Hadisi. Don haka bai yiwuwa batatan bayan Ubangiji da Manzonsa sun yanke wani Hukunci na Halasci ko Haramci akan wani abun a sami wani mutum daban ya tashi wannan Hukuncin, da fadar sa Ubangiji Madaukakin Sarki:

"وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ وَلاَ مُؤْمِنَةٍ إِذَا قَضَى الله وَرَسُولُهُ أَمْرًا أَنْ يَكُونَ لَهُمُ اْلخِيَرَةُ مِنْ أَمْرِهِمْ وَمَنْ يَعْصِ اللهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ ضَلَّ ضَلاَلاً مُبِينًا"                        (الأحزاب – آية 36)

Ma'ana:

"Kuma baya taba yiwuwa ga Mumini ko Mumina idan Ubangiji da Manzon sa suka Hukumta wani lamari suce ga wani zabin (Hukumcin) ba nasu ba, duk wanda ya sabawa (Hukumci ko maganar) Ubangiji da Manzon sa to hakika wannan Mutum ya bata Bata mabayyani". (Ahzab:36)

AURE A SHARI'AR MUSULUNCI

Aure a mahangar Shari'ar Musulunci ya kasu kashi biyu:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next