Shimfida Da Gabatarwa



SHIN AN SHAFE HUKUNCIN AUREN MUTU'A?

Malamai da daman gaske na Makarantar Halifofi (Ahlus-Sunna) sun tafi akan an shafe hukuncin auren Mutu'a, don tabbatar da matsayin Halifa na biyu Umar dan Haddabi. Wasun su suka ce: an shafe hukuncin Mutu'a daga Kur'ani mai tsarki, wasu kuwa suka ce: an shafe ta ne da Sunnar Manzon tsira (Sallallahu alaiHi wa Alihi), sai bangare na biyu suka saba akan maganganu masu yawa:

Amma maganar su da suke cewa an shafe hukuncin Mutu'a da Al-Kur'ani. Suna kafa hujja ne da wannan Aya da Ubangiji Madaukakin Sarki yake cewa:

"وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ, إِلاَّ عَلَى أَزْوَاجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانِهِمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ, فَمَنِ ابْتَغَى وَرَاءَ ذَلِكَ فَأُولَئِكَ هُمُ اْلعَادُون."            (المؤمنون – آية 6-7 )

Ma'ana:

"Kuma sune wadanda suke kare Al'aurar su (daga yin Jima'i da Mace) sai dai ga Matayen su ko kuma Kuyangin da suka mallaka to su ba ababen zargi bane, wanda kuwa ya nemi wanin haka to sun zamo masu ketare iyaka". (AL-mu'minuna: 6-7).

To amma abin lura anan shine, su wadannan Ayoyin guda biyu sun sauka ne a Makka, ita kuwa Ayar dake Magana kan Mutu'a ta sauka ne a Madina. Kuma abinda ya riga sauka baya shafe wanda yazo daga baya. Sannan ita Mutu'a aure ne, shi kuma wanda ake Mutu'ar dashi mace ce, don haka bazai yiwu a gwama wadannan Ayoyi guda biyu da Ayar dake Magana akan Mutu'a ba har ace maganar shafewa ta inganta.

Akwai kuma maganar da suke kawowa ta shafe Mutu'ar da Ayar Idda inda Allah yake cewa:

"فَطَلِّقُوهُنَّ لِعِدَّتِهِمْ"

Ma'ana:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next