Shimfida Da Gabatarwa



"Kuma (Annabi Muhammadu) baya magana ta son rai, dukkanin maganar Sa Wahayi ce da aka yi maSa".

Da wannan Ayar:

"وإنك لعلى خلق عظيم" (القلم: 4)

Ma'ana:

"Kuma lallai hakika Kana kan halayen kirki manya".

Menene ya sami irin wadannan maganganu (na umarni da hanin Mutu'a) suke fitowa a bayan zamanin Sahabbai ya shude? Don me yasa shi Umar dan Haddabi din tun lokacinsa bai yi shaida da dayan su ba yayin da ya hana Mutu'ar. Hakika abinda yake a fili shine da ya kasance a hannunsa akwai wanin wadannan Hadisan da ya kawo shi. Sananne ne cewa ya kawo wa Halifa Abubakar Hadisai na Manzon Allah (Sallallahu alaiHi wa AliHi) kan hanin Yakin duk wanda ya shaida da kalmomin Shahada biyu, yayin da yake Yakin wadanda suka hana Zakka. To me yasa a wannan bai zo da daya daga cikin Hadisan da ake cewa sun shafe Mutu'ar ba kamar yadda suke fada? Ko kuwa su masu kawo irin wadannan maganganu sun fi Sahabbai da Umar dan Haddabi sanin Tarihin Annabi (Sallallahu alaiHi wa AliHi) ne?!

Halifa na biyu (Umar dan Haddabi) bai zamo wadatacce akan haka ba, sai dai kawai yayi gaggawar hukunci ne, don kuwa Musulmi da Sahabbai basu amince da abinda Halifa Umar ya yanke ba sai ma Raddi da sukayi masa. Domin sun san zamanin Manzon tsira (Sallallahu alaiHi wa AliHi) da Abubakar sarai, da ace akwai wani hani to bazai taba buyar musu ba da sun sanshi.

Sannan su kansu wadannan maganganu (na an shafe) suna inkarin maganar Halifa na biyun ne kansa. Domin kuwa cewa yayi shi:

"متعتان كانتا على عهد رسول الله (ص) أنهى عنهما وأعاقب عليهما متعة النساء ومتعة الحج"

Ma'ana:

 

index

next

 



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12