Saukar Wahayi



Bayan nan ne annabin girma da daraja ya koma zuwa ga iyalansa yana mai dauke da wannan nauyi da ya kasance yana jiransa.

Imam Al-hadi (A.S) yana cewa:

Yayin da manzo (S.A.W) ya bar fatauci zuwa Sham kuma ya yi sadaka da dukkan abin da Allah ya arzuta shi da shi na dukiya, ya kasance yana tafiya kogon hira kowace rana yana hawa kansa yana duba zuwa ga ni’imomin rahamar Allah, da kuma nau’in kayatarwar rahamarsa da kyawawan hikimominsa, yana mai duba zuwa ga sama da kuma gefen kasa, da koguna, da dazuzzuka, da sasanni, yana mai tunawa ga ubangiji da wadannan ni’imomi, yana kuma bauta ga Allah hakikanin bauta.

Yayin da ya kai shekara arba’in sai Allah ya kalli zuciyarsa ya ga ita ce mafi kamalar zuciya, mafi haskenta, mafi biyayya, mafi tsoron Allah, mafi kaskan da kai, sai ya yi umarni aka bude kofofin sama Muhammad yana kallo zuwa garesu, kuma ya umarci mala’iku suka sauka yana ganinsu, kuma ya yi umarni da saukar da rahama daga kasan al’arshi zuwa kansa, ya ga Jibril dawisun mala’iku (A.S) yana mai damfare da haske; ya sauka gareshi ya kama damtsensa ya girgiza[2] ya ce: ya Muhammad! Ka karanta, ya ce: me zan karanta? …  (Ya karanta masa surar alak har zuwa aya ta biyar).

Sai ya yi wahayi gareshi da abin da Allah ya yi masa wahayi sannan sai ya hau sama.

Muhammad (S.A.W) ya sauka daga dutse, girman ubangiji ya riga ya mamaye shi, kuma zazzabi mai zafi ya same shi… ga tsoro mai tsanani ya kama shi na gudun kada kuraishawa su karyata shi a labarin da zai ba su, su kuma danganta shi da hauka, kuma da cewa shaidanu suna bujuro masa, alhalin ya kasance tun farko shi ne mafi hankalin halittar Allah, ma fi girman halittunsa, ma fi kin abu a wjansu shi ne shaidan da kuma ayyukan mahaukata da zantuttukansu.

  Sai Allah ya so ya yalwata kirjinsa, ya kuma karfafi zuciyarsa, ya sanya duwatsu da rairayi da kwararo suka yi magana, duk abin da ya hadu da shi daga cikinsu sai ya kira shi ya ce masa: Aminci ya tabbata gareka ya Muhammad, aminci ya tabbata gareka ya masoyin Allah, aminci ya tabbata gareka ya manzon Allah, ka yi albishir, Allah ya fifita ka, ya kawataka, ya adontar da kai, kuma ya girmama ka akan sauran talikai gaba daya na farko da na karshe, kada maganar kuraishawa na cewa kai mahaukaci ne ya bakanta maka rai, ko fadinsu na cewa; kai ka fitinu daga addini, domin mai fifiko shi ne wanda Allah ya fifita.

  Kada kirjinka ya yi kunci don karyatarwar kuraishawa da wawayen larabawa gareka, da sannu ubangijinka zai ba ka matsayin mafi daukakar karamomi, kuma ya daga ka zuwa mafi daukakar darajoji, kuma ya ni’imta masoyanka, ya faranta masu rai da wasiyyinka Ali dan Abu Talib (A.S), kuma ya yada iliminka a cikin bayi da garuruwa da mabudanka da kuma kofar birnin hikimarka: Ali dan abu Talib, kuma da sannu Allah zai sanyaya idanunka da â€کyarka Fatima (A.S), da sannu za a fitar daga gareta da kuma daga Ali (A.S); (â€کya’ya) Hasan da Husain (A.S) shugabannin samarin aljanna, da sannu Allah zai yada addininka a duniya, kuma ya girmama ladan masoyanka da kai da dan’uwanka, da sannu zai sanya tutar yabo a hannunka sai ka sanya shi a hannun dan’uwanka Ali (A.S) sai duk wani annabi da siddiki da shahidi ya zama a karkashinsa, ya kuma zama jagoransu gaba daya zuwa aljannar ni’ima.

AbinLura

Zan so in yi nuni da cewa manzo (S.A.W) ba ya ji tsoron mala’ika ba ne kamar yadda wasu suke kawowa, abin da yake jin tsoro shi ne kada shaidanu su bata kiran, ta hanyar bata shi, ko kuma bata hanyoyin kiransa. Amma sauran bayanai da darussa muna iya barin mai karatu da ruwaya domin ya yi nasa tunani.

Marubuci: Hafiz Muhammad Sa'id

www.hikima.org

hfazah@yahoo.com


[1] - Almizan: 20/327.

[2] - Biharul anwar: 18/207-208.

 



back 1 2